Anver Versi
Anver Versi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Nairobi, |
Karatu | |
Makaranta |
University of Warwick (en) King's College (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Anwarali Versi, wanda aka fi sani da Anver Versi, ɗan jarida ne, haifaffen ƙasar Kenya wanda shine babban editan mujallar New African, da ke London. [1] Ya fara aikin jarida ne a birnin Nairobi, kafin ya koma Ingila, inda a karshe ya yi aiki da wallafe-wallafen da dama na Birtaniya, [2] ciki har da a mujallun; African Business da African Banker . [3] [4] Sauran jaridu da yake wa rubuta sun haɗa da; The Times, The Independent, The Wall Street Journal, Chicago Tribune da International Herald Tribune . [1] [5]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a Nairobi, Kenya, Versi ya fara karatunsa a Makarantar Aga Khan, Mombasa,[6] inda ya karanci fannin, Kimiyyar Siyasa, Tattalin Arziki, da Turanci a Jami'ar Nairobi.[7] Ya tafi domin ƙaro karatu a Jami'ar Warwick da Kwalejin King, Cambridge, duk a London.[3]
Versi ya fara aikinsa a matsayin ɗan jarida yana aiki tare da Ƙungiyar Jaridun Nation a Nairobi, kafin ya koma Landan a 1983, inda ya kasance babban editan jaridar The Guardian da Financial Times, sannan kuma mujallun Afirka dake a Burtaniya sun ɗauke shi aiki a jaridar Afirka Journal da Drum (Afirka ta Yamma). Ya kashe fiye da shekaru 30 yana aiki tare da kamfanin IC Publications, [4] shi ne editan da ya kafa mujallar African Banker, [2] kuma a cikin shekara ta 1994 ya zama edita a jaridar African Business haka-zalika a shekarar 2018 shine babban editan mujallar New African (jaridar da ya taɓa zama mataimakin editan jaridar daga shekara ta 1983 zuwa 1994). [7]
Cigaba da karutu
[gyara sashe | gyara masomin]- Football in Africa, Collins, 1986, 08033994793.ABA
- Search for Africa's Political Identity, Macmillan
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Anver Versi, Editor-In-Chief of New African, Interviews His Highness The Aga Khan – 'A Man For All Seasons'", Barakah, 23 September 2019.
- ↑ 2.0 2.1 "Anver Versi | Editor African Business and African Banker magazines", Oracle.
- ↑ 3.0 3.1 "Anver Versi, Editor of African Business Magazine", ReConnect Africa.
- ↑ 4.0 4.1 "Anver Versi, former Editor, African Business", African Business, 23 January 2015.
- ↑ "Anver Versi" Archived 2019-12-21 at the Wayback Machine at Brand Africa.
- ↑ Versi, Anver (June 2018). "A Man for All Seasons"". New African. No. 584. Retrieved 12 May 2022.
- ↑ 7.0 7.1 Brandrup-Lukanow, Assia (14 December 2012). "In Honour Of A Great Journalist". New African.