Arewacin Cyprus
Arewacin Cyprus | |||||
---|---|---|---|---|---|
Kuzey Kıbrıs Türk Cumhuriyeti (tr) | |||||
|
|||||
| |||||
Take | İstiklâl Marşı (en) | ||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Territory claimed by (en) | Cyprus | ||||
Babban birni | North Nicosia (en) | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 390,745 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 116.47 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turkanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 3,355 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Turkish Federated State of Cyprus (en) | ||||
Ƙirƙira | 1983 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Gangar majalisa | Assembly of the Republic (en) | ||||
• President of Northern Cyprus (en) | Ersin Tatar (en) (23 Oktoba 2021) | ||||
• Prime Minister of Northern Cyprus (en) | Ünal Üstel (en) (12 Mayu 2022) | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi | Turkish lira (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC+02:00 (en)
| ||||
Suna ta yanar gizo | .tr (mul) | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +90 | ||||
Lambar taimakon gaggawa | *#06# |
Arewacin Cyprus ( Turkish ), a hukumance Jamhuriyar Turkiyya ta Arewacin Cyprus ( TRNC ; Turkish , KKTC ), yanki ne na zahiri a arewacin rabin tsibirin Cyprus. Mutane dubu ɗari uku suna rayuwa a cikin 3,335 km² Turkiyya ce kaɗai ƙasar da ta amince da yankin a matsayin jamhuriya mai cin gashin kanta duk da takunkumin ƙasa da ƙasa da ake sakawa.
An ci Cyprus da yaƙi kuma ta zama wani ɓangare na Daular Usmaniyya daga shekarar 1570-1914. Turkawa da yawa sun zama baƙi . Yayin da Daular Ottoman ta goyi bayan daular Birtaniyya a yaƙin duniya na daya, Turawan Burtaniya suka mamaye Cyprus. A cikin 1923, ta Yarjejeniyar Lausanne Turkiyya ta ba da tsibirin ga Masarautar Burtaniya wanda a cikin 1925 ya mai da shi ya zama masarautar mallaka . Birtaniyyawan sun mallake shi daga 1878 har zuwa 1960.
A cikin 1974, don mayar da martani ga wani rikici da ke ƙaruwa da Girka, sojojin Turkiyya sun mamaye Cyprus. Yawancin baƙi daga asalin Turkiyya sun fito daga Turkiyya zuwa arewacin tsibirin. Wannan matakin ya jawo Allah wadai daga kasashen duniya kuma Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da Arewacin Cyprus ba.
Tun daga shekarar 1974, Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa layin tsagaita wuta tsakanin Tsibirin Cyprus na Turkiya da Girkawan Cyprus. An kafa '' Jamhuriyar Turkiyya ta Arewacin Cyprus '' a cikin 1983 kuma Rauf Denktash ya zama shugaban ƙasa na farko. An gudanar da shawarwari game da hadadden tsibiri sau da yawa ba tare da nasara ba.
Arewacin Cyprus, duk da matsayin da take da shi na kasashen duniya, ya yi fice a tsakanin sauran yankunan "daskararrun rikice-rikice" kamar yadda yake da kyakkyawan tsarin mulki na dimokiradiyya tare da manyan matakan 'yanci na siyasa da kuma shiga tsakani a harkar siyasa.
Sauran yanar gizo
[gyara sashe | gyara masomin]- Zypern Times
- Nordzypern Almanac
- Arewa Cyprus Information Map Archived 2007-06-17 at the Wayback Machine Archived - Littafin adireshi da tushen bayanai ga Arewacin Cyprus. Bayanin kamfanin ciki har da taswirar wuri. Tambayoyi na musamman da takamaiman wuraren zama da masu yawon bude ido
- Gwamnatin TRNC