Asibitin Koyarwa na Jami'ar Olabisi Onabanjo
| Bayanai | |
|---|---|
| Suna a hukumance |
Olabisi Onabanjo University Teaching Hospital |
| Iri |
university hospital (en) |
| Ƙasa | Najeriya |
| Harshen amfani | Turanci |
| Mamallaki | Jami'ar Olabisi Onabanjo |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | 1986 |
| oouth.com… | |
Asibitin Koyarwa na Jami'ar Olabisi Onabanjo (OOUTH), (wanda ake kira da, Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Ogun (OSUTH), yana cikin Sagamu, Jihar Ogun, Kudu maso Yammacin Najeriya.[1] An kafa asibitin koyarwa ne a shekarar 1986 da manufar koyar da ɗaliban likitanci daga jami’ar Olabisi Onabanjo da kuma samar da ayyukan kiwon lafiya ga ƴan asalin jihar Ogun da Najeriya baki ɗaya.[2]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]
An kafa OOUTH a ranar 1 ga watan Janairu, 1986, tare da haɗin gwiwar Kwalejin Kiwon Lafiyar Kwalejin Obafemi Awolowo don ba da horon likitanci ga ɗaliban da ke karantar aikin likitancin a Jami'ar Olabisi Onabanjo. Asibitin koyarwa ya kasance a tsohon asibitin jihar, Sagamu, jihar Ogun, Najeriya. Babban Daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin shi ne Farfesa. AAO Laditan[3]. Majalisar gudanarwar da gwamnatin jihar ta naɗa ne ke kula da asibitin.[4] Ya zuwa shekarar 2016, shugaban majalisar gudanarwar shine Farfesa Emmanuel O. Otolorin.[5]
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "We will return OOUTH to its glorious days ― Coker". Vanguard News (in Turanci). 2020-12-19. Retrieved 2022-04-22.
- ↑ "Restoring Olabisi Onabanjo Varsity Teaching Hospital's Past Glory". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-09-25. Retrieved 2022-04-22.
- ↑ https://ha.m.wiktionary.org/wiki/asibiti
- ↑ Dimeji Kayode-Adedeji. "ogun appoints new governing council oou teaching hospital". Premium Times. Retrieved 1 February 2016.
- ↑ welcome Archived 2019-12-05 at the Wayback Machine, Olabisi Onabanjo University Teaching Hospital, Retrieved 27 February 2016