Jump to content

Ayo Oke

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ayo Oke
Director General of the National Intelligence Agency of Nigeria (en) Fassara

7 Nuwamba, 2013 - Oktoba 2017
Rayuwa
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya

Ayo Oke shine tsohon babban darakta na hukumar leken asirin Najeriya (NIA), wanda shugaban kasa na wancan lokacin Goodluck Jonathan ya nada a ranar 7 ga Nuwamba 2013.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ayo Oke a jihar Oyo.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Oke ya taba zama Darakta (Yankuna) a hedikwatar hukumar ta NIA, kuma kafin hakan shi ne jakadan Najeriya a Sakatariyar Commonwealth da ke Landan. Ya gaji Ezekiel Olaniyi Oladeji a matsayin darekta janar na Hukumar Leken Asiri ta Najeriya a watan Nuwamban shekarar 2013.

Dakatarwa da sallama[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Afrilu na shekarar 2017, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Oke bayan da jami’an yaki da cin hanci da rashawa daga Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati suka gano sama da dalar Amurka miliyan 43 (£ 34m) a cikin wani gida a Osborne Towers, Ikoyi, Lagos . A ranar 30 ga Oktoba, daga karshe shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kori Oke bayan nazarin rahoton kwamitin binciken da Mataimakin Shugaban ya jagoranta. [1]

Bayani[gyara sashe | gyara masomin]

  1. ^ a b
  2. ^
  3. ^
  4. ^
  5. ^ http://sunnewsonline.com/breaking-buhari-sacks-babachir-lawal-ayo-oke-appoints-mustapha-new-sgf/
  1. http://sunnewsonline.com/breaking-buhari-sacks-babachir-lawal-ayo-oke-appoints-mustapha-new-sgf/