Jump to content

Bashir Aliyu Umar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Bashir Aliyu Umar Malamin addinin Musulunci a Najeriya (an haife shi ranar 27, ga watan Yuli a shekarar 1961) a Unguwar Yola dake kwaryar jihar Kano.[1]

Malam Bashir ya fara da karatun Allo har lokacin da ya samu damar saukar Alqur'ani mai girma. Bayan ya sauke Alqur'ani ya cigaba da neman Ilimin addinin Musulunci inda yayi karatu a wajen malamai daban-daban duka a cikin birnin Kano. Yayi karatun firamare a firamaren Jar Ƙasa, bayan gama karatun firamarensa yayi makarantar sakandare a kwalejin gwamnatin tarayya Federal Government Collage Kano. Ya karanta Injiniyan lataroni (Electrical Engineering) a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya. Yayi karatun addinin Musulunci a Jami'ar Musulunci ta Madina inda ya karanta Ilimin Hadisi.

Barin Jami'ar Ahmadu Bello Zariya

[gyara sashe | gyara masomin]

An kori Bashir tare da wasu ɗalibai daga jami'ar Ahmadu Bello Zariya saboda yunƙurin da Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai ta MSSN a jami'ar ta yi na hana shan giya a jami'ar duk da hukumomin makarantar sun ba da damar shan giya a cikin makarantar.[2]

Bashir Aliyu Umar an haife shi a cikin garin kano dake a arewancin nageriya ɗa ne ga Mai girma Ɗan Amar ɗin kano.

Lakcara ne a jami'ar Bayero dake Kano, wanda daga baya gwamnatin kano ta gayyace shi domin zama Sakatare na Din-din-din a ma'aikatar Shari'ah ta jihar. Mamba ne a Commitee na harkar tattalin arziki na musulunci a JA'iz Bank, yayi aiki a matsayin Shugaba na Mashawarta na Addinin musulunci a Bankin Stanbic IBTC Najeriya, kuma yanzu haka mamba ne na Shari'ah Commitee of the International Islamic Liquidity Management Corporation.

  1. "Ku San Malamanku Tare da Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar". bbc.hausa.com. 25 December 2020. Retrieved 24 June 2024.
  2. "Ku San Malamanku Tare da Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar". bbc.hausa.com. 25 December 2020. Retrieved 24 June 2024.