Jump to content

Battle of Kwatarkwashi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentBattle of Kwatarkwashi
Iri faɗa
Kwanan watan 27 ga Faburairu, 1903
Wuri Jihar Zamfara
Participant (en) Fassara

Yaƙin Kwatarkwashi wani gagarumin yaƙi ne tsakanin Turawan mulkin mallaka na Arewacin Najeriya da kuma sojojin masarautar Kano ta Khalifancin Sakkwato . Kashin da sojojin dawakan kano suka yi a yanƙin ya nuna yadda masarautar Kano ta kaure .

A cikin shekarar 1899, Lord Lugard ya shelanta mulkin mallaka na Birtaniyya a kan yawancin Daular Sokoto. Tare da gazawar diflomasiyya da yawa ga Halifa, a cikin shekarar 1900 aka ƙaddamar da yaƙin soja don murkushe halifanci. a lokacin da labarin yaƙin Kano da fadowar kagara ya iso Sokoto a watan Fabrairun shekarar 1903, sai sojojin dawakan Kano suka yi tattaki domin ƙwato garin.[1]

Bayan arangama guda uku da suka yi da sojojin Birtaniya a baya, wani katon Sojan Birtaniya daga Kano ya yi wa sojojin Kano kwanton ɓauna a manyan duwatsun Kwatarkwashi. Bayan an shafe sa'o'i 6 ne aka yi arangama, rasuwar Wazirin Kano ya sa sauran sojojin dawaki suka koma Sokoto, wani ɓangare mai tsoka na rundunar amma a ƙarƙashin Muhammad Abbas ya miƙa wuya ga turawan Ingila ya koma Kano.[2]

A Kano aka kuma naɗa Muhammad Abbas Sarkin Kano. Dakarun dawakan Kano na ƙarshe sun haɗe cikin rundunar Halifa ta Sakkwato.

  1. "Fall of Kano". West Gippsland Gazette. 19 May 1903. p. 6 – via National Library of Australia.
  2. Ikime, Obaro (1977). Fall of Nigeria. Heinemann. ISBN 0435941402.