Jump to content

Bendtner

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bendtner

Bendtner An haifeshi a ranar goma sha shida ga watan Junairu shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas 1988. Ya kasance tsohon dan wasan kasar Danish ne. Kuma ya kasance kwararren dan wasa ne da yake doka gaba wato wurin kai farmaki na tsakiyar gaba. Sai dai a wasu lokutan yakan buga gefen dama idan ta kama kuma yana buga gefen hagu. A takaice dai babu inda dan wasan baya bugawa a fannin gaba. Sannan kuma dan wasa ne mai karfin gaske sosai kuma mai wahalar tarewa. Dan wasan yana da babbar kwarewa a saman iska inda ya kware sosai a wajen sanya ma kwallo kai.

Bayan nasarori daya samu tun lokacin kuruciya kungiyoyi da dama kamar kungiyar kwallon kafa ta Tarnby Boldklub Kjobenhavns Boldklub sa kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Bendtner din ya rattaba hannu a matsayin kwararren dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar alif dubu biyu da biyar 2005. Dan wasan ya fara halatta a watan Oktoba shekara ta alif dubu biyu da biyar 2005 a wasan kofin lig wanda aka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Sunderland a shekarar. A shekarar alif dubu biyu da shida 2006 zuwa shekara ta alif dubu biyu da bakwai 2007, yaje zaman aro a kungiyar dake buga Championship wato kungiyar kwallon kafa ta Birmingham city. Inda ya buga wasanni har guda Arba'in da takwas 48.

Bayan dawowarsa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal din, dan wasan ya shigo cikin sha dayan farko inda ya shigo cikin jerin masu buga wasanni kullum. Sai dai kuma dan wasan ya fara rasa damar sa a shekarar alif dubu biyu da goma sha daya 2011 zuwa shekara ta alif dubu biyu da goma sha biyu 2012. Hakan ne yasa ya kara tafiya wani zaman aron insa ya shafe kusan duk shekarar a zaman aro inda ya koma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sunderland inda ya bugama kungiyar wasanni har guda talatin da takwas 38. Dan wasan ya shafe duka rayuwar kwallon shi ta shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2012 zuwa shekara ta alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 a zaman aro da kungiyar kwallon kafa ta Juventus inda ya bugama kungiyar wasanni guda goma 10 amma ba tare da ya zura kwallo a raga ba.

Bendtner ya raba gari da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar alif dubu biyu da goma sha hudu 2014 inda ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Vfl Wolfsburg a matsayin dan wasan kyauta inda ya samu nasarar jefa masu kwallo wadda ta basu nasara a gasar kofin Dfl super cup. Sun sakeshi a shekarar alif dubu biyu da goma sha shida 2016 inda ya koma gasar Premier league a kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest inda suke buga gasar Championship a shekarar. A watan Match shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017 ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafan Rosenberg.

A fannin kasa kuma dan wasan yana wakiltar kasar shi ta haihuwa wato Denmark inda ya wakilci kasar tashi a lokuta da dama da kuma gasanni da dama inda ya wakilci kasar tun Yana dan karamin yaro. Dan wasan ya wakilci kasar cikin tawagar yan kasa da shekaru goma sha shida U16, sannan ya wakilci kasar a cikin tawagar yan kasa da shekaru goma sha bakwai U17, kuma hada shi a cikin tawagar yan kasa da shekaru goma sha tara U19 sai kuma tawagar yan kasa da shekaru ashirin da daya 21. Sai kuma yaje babban mataki inda ya wakilci kasar a matsayin kwararren dan wasa. Inda ya fara wakiltar kasar tashi tun yana dan shekara goma sha takwas 18 a ranar goma sha shida 16 ga watan Ogusta shekarar alif dubu biyu da shida 2006 inda suka doka wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta kasar Poland inda ya samu nasarar jefa kwallon sa ta farko a wasan.

Dan wasan yana cikin jerin yan wasan da suka halarci gasar kofin duniya. Haka zalika dan wasan ya wakilci kasar tashi a gasar Euro 2012 daa aka buga da kuma kofin duniya da aka buga a shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas 2018.

Salon Wasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bendtner dan wasa ne mai hazaka da zai iya buga ko ina a gaba. Kasancewar shi dan gaban tsakiya yana amfani sosai wajan buga sauran wuraren suma. Kasancewar shi dogo kuma kakkarfa maji karfi, yana amfani da wannan damar domin danne yan baya kuma yana da tsalle tsalle da tashi hakan ne ya bashi damar cin kwallaye da kai. Dan wasan yana da kwarewa sosai a saman iska kuma yana da karfin bugun kwallo da kai.

Dukda cewa yana da alkawari, amma dan wasa ne marar tarbiya a yarintar kwallon sa. Dan wasa ne da yake da abubuwa masu yawa a cikin salan wasannin sa. Yana da basira, sauri da zafin nama, taba kwallo sau daya, jajircewa, cin kwallo da kuma taimakawa aci.

Tsohon kwararren kocin dan wasan wato Arsene Wenger ya bayyana dan wasan a matsayin gwarzo kuma kwararren da gaba. A cewar tsohon kocin, Bendtner dan gaba ne mai hatsari sa ka iya cin ƙwallo ta ko wane hali kuma a inda yake bukata.

Saidai dan wasan yayi fama da raunuka daban daban inda yasha jinya sosai a lokuta da dama wanda hakan ya bada gudummawar hana dan kwallon yakai matakin da yake bukata.

Manzarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://en.wikipedia.org/wiki/Nicklas_Bendtner

"Nicklas Bendtner". Barry Hugman's Footballers. Retrieved 14 April 2017.

"Player Profile: Nicklas Bendtner". Vfl Wolfsburg. Archived from the original on 5 November 2014. Retrieved 4 February 2015.