Benjamin Campbell (wakilin ofishin jakadanci)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Colony a Sierra Leone

Benjamin Campbell (wakilin ofishin jakadanci)
Rayuwa
Haihuwa 1802
ƙasa United Kingdom of Great Britain and Ireland
Mutuwa Lagos, 17 ga Afirilu, 1859
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Campbell mazaunin Colony a Sierra Leone kuma dan kasuwa na yankin kogin Nunez, Guinea.A can ya kasance memba na Majalisar Mulkin Mallaka ta Sierra Leone don haka aka ba shi lakabin 'Mai daraja' wato Honourable .A cikin shekarar 1841 an samu takardu a cikin Segunda Rosario,wani jirgin ruwa da ake zargin anyi cinikayyar bayi dashi. Wanda akai watsi dashi wa hukuncin kotun Havana Mixed Commission. Wannan ya haifar da damuwa cewa Campbell yana da hannu a cinikin bayi. Lokacin da aka binciki Campbell daga baya, ya amsa cewa ya kasance yana kasuwanci tare da Niara Bely(aka Isabela Lightbourn) tsawon shekaru goma sha shida amma dangane da halaltattun kayayyaki kamar su hauren giwa,fatu, kakin zuma, zinare da kofi.Ko da yake Misis Lightbourn ita ma ta yi cinikin bayi, amma Campbell ya musanta hannu a kai, kuma ya yi iƙirarin cewa ya sha asara na kashin kansa bayan lalatar da dukiyarsa da aka yi a kogin Nunez, saboda adawa da cinikin bayi.:21

An nada shi a matsayin Consul a Legas a ranar 21 ga Yuli 1853 kuma ya yi aiki a wannan mukamin har zuwa rasuwarsa a ranar 17 ga Afrilu 1859.

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]