Brely Evans

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Brely Evans
Rayuwa
Haihuwa Oakland (en) Fassara, 9 Disamba 1972 (51 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta Skyline High School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Jarumi, dan wasan kwaikwayon talabijin, ɗan wasan kwaikwayo, mawaƙi da cali-cali
IMDb nm3858768
brelyevans.com
Niecy Nash, LeRoy Mobley and Brely Evans

Brely Evans (an haife ta ranar 9 ga watan Disamban shekarata 1972). 'yar fim ce Ba'amurkiya, mawaƙiya, marubuciya, mawallafiya, kuma mai shirin ban dariya ce. Ta kasance tauraruwa a cikin fina-finai da yawa, kuma a cikin shekarar dubu biyu da tara (2009) ta yi fice a cikin Oprah Winfrey Network prime time soap opera Ambitions .

Rayuwa da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Evans sannan kuma ta girma a Oakland, California . Matsayinta na zamanta fitacciyar yar fim ya fara ne a lokacin da fito a shekarar 2010 a wani fim din sha'awa da barkwanci mai suna Just Wright wanda ta fito a matsayin Sarauniya Latifah . A shekarar 2012, ta fito a fim main suna Sparkle . Sauran kyaututtukan fim dinta sun hada da Mine Not Yours (2011), David E. Talbert Suddenly Single (2012), Black Coffee (2014), The Man in 3B (2015), da kuma jagoran rawar data takar a cikin You Can't Fight Chrismas (2017) ).

A talabijin, Evans tana da maimaitaccen matsayi a jerin wasan kwaikwayo na BET Being Mary Jane da kuma a TV jerin wasannin barkwanci na Born Again Virgin . A cikin shekarar 2019, an dauwamar da Evans a wani matsayi a cikin jeri biyu na wasannin yau da kullum. Na farko, jagoran mata a jerin wasan barkwanci na Bounce TV Last Call Opposite Charles Malik Whitfield . Daga baya kuma a wannan shekarar, ta fara zama tauraruwa a cikin shirin Oprah Winfrey Network prime time soap opera, Ambitions ta fito a matsayin Rondell Lancaster, 'yar'uwar Magajin Garin Atlanta Evan Lancaster ( Brian J. White ). An soke jerin shirin bayan anyi yanayi guda daya. A cikin shekarar 2020, ta bayyana a karo na biyu na wasan kwaikwayo na aikata laifi na BET The Family Business, kuma ta yi fice a cikin Urban Movie Channel mai ban dariya-jerin wasan kwaikwayo For the Love of Jason da Terror Lake Drive .

Bayani[gyara sashe | gyara masomin]

 

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]