Callum Hudson-Odoi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Callum Hudson-Odoi
Lewes 0 Chelsea DS 1 Pre Season 22 07 2017-599 (36103251735) (cropped).jpg
Rayuwa
Cikakken suna Callum James Hudson-Odoi
Haihuwa Wandsworth (en) Fassara, 7 Nuwamba, 2000 (20 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Karatu
Makaranta Whitgift School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Chelsea F.C.2017-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 20
Tsayi 182 cm

Callum James Hudson-Odoi (an haife shi a 7 November 2000) Ɗan'wasan ƙwallon ƙafar ƙasar ingila ne, wanda ke buga wasan gaba ko gefe a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kulub din Chelsea.

Lokacin dayake Chelsea academy, Hudson-Odoi yana daga cikin yan'wasan da suka lashe U18 Premier League a shekarar 2017 da kuma lashe FA Youth Cup har sau biyu ajere. Sanadiyar ƙarin ƙoƙarinsa a ƙungiyar rukunin matasa cikin watan January 2018 aka kaisa ga gurbin yan'wasa kwararru, tun daga nan yayi wasa fiye da 20 a club.

Hudson-Odoi ya kuma samu kokari da dama a ƙungiyar rukunin matasa a England, wadanda sune suka kasance na biyu a UEFA European Under-17 Championship da kuma samun lashe FIFA U-17 World Cup a wannan shekarar. A watan Maris 2019, yazama dan'wasa mafi karancin shekaru daya fara buga wasan gasa ma ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar England, inda yabuga wasan tsakanin UEFA Euro 2020 qualifiers da ƙasar Czech Republic.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan Muƙalar guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyara shi.