Cecilia Omaile Ojabo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Cecilia Omaile Ojabo (an haife ta a shekara ta 1960) tsohuwar kwamishiniyar lafiya ce a jihar Benue, Najeriya. Gwamna Samuel Ortom ne ya rantsar da ita a shekarar 2015. Ita kuma mataimakiyar farfesa ce a fannin ilimin ido a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Benue (BSUTH).[1] A matsayinta na kwamishiniya ta yi kokarin inganta harkar lafiya a yankunan karkarar jihar Benue. Ta kuma yi aiki don ganin asibitoci sun kasance masu aiki; karuwar yawan ma'aikatan lafiya; da kuma kawar da cutar shan inna da bullar cutar kwalara a fadin jihar.[2]

Rayuwar farko da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ta halarci makarantar firamare ta Saint Francis, Otukpo, Najeriya, daga shekarun 1965 zuwa 1971, sannan ta wuce Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati, Shendam, Najeriya, inda ta kammala karatu da takardar shedar Makarantar Yammacin Afirka a shekarar 1976. Ta sami digiri a fannin likitanci a Jami'ar Benin a 1985. Ta yi aiki a asibitoci da dama a Najeriya da Scotland.[3][4][5]

Ita mamba ce ta West African College of Surgeons.[6]

Ta kasance Kwamishiniyar Lafiya da Ayyukan Jama'a a Jihar Binuwai daga shekarun 2015-2018.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Prince Joshual. "Govt should address grassroots healthcare — Ojabo | Champion Newspapers Limited". Championnews.com.ng. Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2016-01-11.
  2. "'Our grassroots healthcare needs urgent attention'". Dailytrust.com.ng. 2015-09-01. Archived from the original on 2016-01-25. Retrieved 2016-01-11.
  3. "Dr. Mrs. Ojabo, Cecelia Omale". Benuestate.gov.ng. 1960-10-03. Archived from the original on 2016-02-20. Retrieved 2016-01-11.
  4. Prince Joshual. "Govt should address grassroots healthcare — Ojabo | Champion Newspapers Limited". Championnews.com.ng. Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2016-01-11.
  5. "Benue House of Assembly Confirms Commissioner Nominees | Welcome To Benue Family Blog". Benuefamily.com. Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2016-01-11.
  6. "Original fellows list" (XLS). West African College of Surgeons.