Samuel Ortom

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samuel Ortom
Gwamnan jahar benue

29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Gabriel Suswam
Minister of Aviation of Nigeria (en) Fassara

14 ga Faburairu, 2014 - 15 ga Augusta, 2014
Stella Oduah
Minister of Industry, Trade and Investment (en) Fassara

11 ga Yuli, 2011 - 25 Oktoba 2015
Rayuwa
Cikakken suna Samuel Ioraer Ortom
Haihuwa Benue, 23 ga Afirilu, 1961 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tiv
Harshen uwa Harshen Tiv
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Matakin karatu Master in Public Administration (en) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen Tiv
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan kasuwa
Kyaututtuka
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa People's Democratic Party (en) Fassara

Samuel Ioraer Ortom saurare; an haife shi a ranar 23 ga watan Afrilu 1961) ɗan siyasan Najeriya ne, kuma ɗan kasuwa, mai gudanarwa kuma mai taimakon jama'a. Ya kasance karamin ministan kasuwanci da saka hannun jari a Najeriya a lokacin mulkin Goodluck Jonathan. An zabi Ortom gwamnan jihar Benue a matsayin dan jam’iyyar All Progressives Congress a shekarar 2015. An sake zaɓen sa a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayu 2019.[1][2][3]

Tarihi da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ortom a ranar 23 ga watan Afrilu 1961 a karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Najeriya. Ya halarci makarantar firamare ta St. John's Gboko a shekarar 1970 amma ya koma St. Catherine's Primary School, Makurdi a shekarar 1974, inda ya kammala karatunsa na firamare a shekarar 1976. Cif Dr. Samuel Ioraer Ortom ya samu gurbin shiga makarantar sakandaren kasuwanci ta Idah, Idah a jihar Kogi a shekarar 1976.[4] Ya yi shekara biyu a makarantar kafin mahaifinsa ya yi ritaya a shekarar 1979 ya kawo karshen burinsa na kammala karatun sakandare saboda kudi. Ya zama kwararren direba.

Daga nan ya samu shaidar kammala karatu da kuma Diploma a fannin tallace-tallace. Ya yi rajista a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya kuma samu shaidar kammala karatun digiri na wucin gadi a shekarar 1995 da kuma Diploma a aikin jarida a 1998. Daga nan ya halarci Jami’ar Jihar Binuwai inda ya sami Difloma mai zurfi a fannin Gudanar da Ma’aikata a shekarar 2001 da kuma Digiri na biyu a fannin Gudanarwa a shekarar 2004. Ortom ya sami Ph.D, daga Jami'ar Commonwealth, Belize, ta hanyar koyan nesa wato distance learning.

Rayuwar Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ortom ya yi aiki da jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Binuwai da suka haɗa da National Center Party of Nigeria a matsayin Sakataren Yaɗa Labarai na Jiha; Ma'ajin Jam'iyyar Jama'a (APP); da Sakataren Jiha da kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jiha. Ya kuma taɓa zama Darakta mai kula da ayyuka na yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Benuwe a shekarar 2007 da kuma daraktan gudanarwa da dabaru na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Goodluck/Sambo a shekarar 2011. Ya kasance mai binciken kuɗi na kasa na PDP kafin a naɗa shi a matsayin Ministan Tarayyar Najeriya a watan Yulin 2011.[5]

A watan Afrilun 2015, ya tsaya takarar gwamnan jihar Benue kuma ya yi nasara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A watan Yulin 2018, Ortom ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress sakamakon rikicin cikin gida na jam’iyyar.

A zaben gwamnan jihar Benue da aka gudanar a ranar 9 ga Maris 2019 da kuma ranar 23 ga watan Maris 2019, an sake zaben Ortom a matsayin Gwamna bayan da ya samu kuri'u 434,473 yayin da Emmanuel Jime na jam'iyyar All Progressive Congress ya samu kuri'u 345,155. Bayan zaɓen, Jime ya kalubalanci nasarar Ortom kuma ya shigar da kara a kan dalilan rashin bin ka’idojin dokar zabe, 2010 da aka yi wa kwaskwarima. A ranar 21 ga watan Junairu 2020 kotun koli ta tabbatar da zaben Samuel Ortom a matsayin gwamnan jihar Benue.

Tallafawa[gyara sashe | gyara masomin]

Ta hanyar kafa gidauniyar Oracle Business Limited, Ortom ya ware kudade a Asibitin St. Theresa, Asibitin Makurdi da Rahama, dake titin Gboko Road, Makurdi, domin jinyar ciwon cizon sauro da cizon maciji kyauta ga marasa lafiya. Gidauniyar ta kuma yi aiki don rage wa fursunonin wahalhalu, yayin da ta kuma bayar da dabaru daban-daban na koyon sana’o’i domin ingantacciyar hanyar shiga cikin al’umma. Makarantar Tuƙi ta Oracle wani shiri ne, wanda ke horar da ƙwararrun direbobi akai-akai.[6]

Kyauta[gyara sashe | gyara masomin]

 

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

A yanzu haka yana da aure da ‘ya’ya ga matarsa Mrs. Eunice Erdoo Ortom.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "It's Official: PDP's Samuel Ortom wins re-election as Benue governor |" . 24 March 2019. Retrieved 24 March 2021.
  2. "Nigerians regret voting for Buhari, APC, says Ortom" . The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News . 21 January 2022. Retrieved 22 February 2022.
  3. "Samuel Ortom Archives - The Nation Newspaper" . thenationonlineng.net . Retrieved 26 February 2022.
  4. Ayado, Solomon (26 September 2014). "Ortom, From Motor Park Tout To A Minister Of The Federal Republic" . Leadership . Retrieved 4 October 2014.
  5. "Benue at 46: Like Winston Churchill, like Samuel Ortom" . TheCable . 4 February 2022. Retrieved 18 March 2022.
  6. "Samuel Ortom – List of Treated Snake Bite Victims and Cost from 2010 – 2013" . Samuel Ortom. Retrieved 26 October 2014.