Charlette N’Guessan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Charlette N’Guessan
Rayuwa
ƙasa Ivory Coast
Sana'a
Sana'a tech entrepreneurship (en) Fassara da marubuci

Charlette N’Guessan matashiya ce da ke zaune a Birnin Accra ta kasar Ghana wacce ta zama abun alfahari ga Afrika a fannin Injiniyanci. [1]

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Charlette N’Guessan ‘yar shekara 26, da ke zama a Ghana ita ce mace ta farko da ta lashe babbar kyautar ta Royal Academy of Engineering, wani babban gasa da aka shirya a 2020 domin baje fasahar kimiyyar Injiniyanci.[2] Bayan kasancewarta ‘yar Afirka ta farko da ta samu wannan kyautar, ta kuma daukaka darajar kasar Ghana na kasancewa ta farko da ta samu kaiwa ga wannan babban matakin. N’Guessan ta lashe kyautar ne saboda fasahar da ta kirkira ta BACE API ita da ‘yan tawagarta, fasahar da ke ganowa da tantance mutane a yayin da ake bukatar hakan. Wannan fasahar an sanya hikima wajen ganin an gano tare da tantancewa ta hanyar fikira da hikima cikin sauki, wanda jama’a da kamfanoni da dama suka gamsu an zuba kwarewa da kokari sosai wajen kirkirar wannan manhajar. Fasahar na iya tabbatar da hoton mutum na asali ko bidiyo da aka dauka a wayoyin salula tare da tantance wanda ake son tantancewa ko ganowa cikin hanzari. Wannan manhajar kai tsaye zai taimaka wa kamfanoni da hukumomi sosai wajen saukake ayyukan da ke gabansu. Na’urar da ta samar, bai bukatar wasu muhimman kayayyaki wajen tafiyar da kansa. Wani abun sha’awa da burgewa da wannan na’urar mai amfani da wayoyin salula ko kwamfutocir da aka samar ba kamar na’urar Global AI Systems ba ne, shi BACE API an samar ne tare da ingantasa wanda zai yi aiki sosai musamman don ‘yan Afrika.[3]

Gasa[gyara sashe | gyara masomin]

N’Guessan a matsayin wacce ta lashe gasar Injiniyanci na Afrika ta samu kyautar fan dubu 25,000.[4] N’Guessan da abokan aikinta ne suka kirkira wannan manhajar a shekarar 2018 bayan sun gudanar da wani dogon bincike wanda ya nuna cewa bankuna a Ghana su na da muhimman matsaloli ta hanyar yanar gizonsu, wanda suke fuskantar masu kutse da ‘yan damfara. Don haka ne suka dukufa binciken hanyoyin da za su taimaka wajen samar da manhajar da zai taimaka wajen shawo kan lamarin. Manhajar BACE API na da damar amfani da Fasfot din ‘yan Ghana da sauran takardu domin amfani da su ta fannin tantancewa da tabbatarwa. An samu wannan nasarar ne sakamakon kyakkyawar hadin guiwa da aka samu da jami’an da ke kula da wannan babin na gwamnatin kasar. An kirkiri fasahar ne domin taimakawa ma’aikatu da kamfanonin da ke dogaro da na’urar tantance mutane. Kuma yanzu haka kamfanoni biyu na kasar Ghana na amfani da manhajar domin tantance kwastamominsu da taskace lamura.[5] Gasar baje kolin fasaha ta Africa Prize for Engineering ya kasance wani babban gaza da masu hasaha suke baje kolinsu domin ganin an samar da wani cigaba da fuskacin kere-kere. Royal Academy of Engineeing da ke kasar UK ce ta kaddamar a shekarar 2014 wanda kuma ake yinsa duk shekara. Lokacin da matashiyar ta samu wannan nasarar, ta samu lambar yabo da jinjina daga bangarori daban-daban ko Ministan Afrika a UK, James Duddridge sai ya nuna jinjiya da ta jarumar matashiyar murnar daukaka Afrika da ta yi bisa nuna hazakar samar da manhajar da zai taimaka wa kasa da kasa wajen rage kaifin matsaloli musamman na ‘yan damfara da masu kutse.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]