Jump to content

Cheremshyna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cheremshyna
Dmytro Hnatyuk (en) Fassara musical work/composition (en) Fassara
Lokacin bugawa 1965
Characteristics
Genre (en) Fassara romance (en) Fassara
Harshe Harshan Ukraniya
Lyricist (en) Fassara Q12173136 Fassara
Other works
Mai rubuta kiɗa Vasyl Mykhailiuk (en) Fassara
External links
YouTube
cheremshyna

"Cheremshyna" ( Ukraine ) waƙar soyayya ce a harshen Ukraine. An fara fitar da waƙar a shekarar 1965, wanda Vasyl Mykhailyuk ya rera wakar shi kum Mykola Yuriychuk ya rubuta ta . Wanda ya fara taka rawar waƙar shine Dmytro Hnatyuk .

Cheremshyna suna ne ga Prunus padus (Bird Cherry) a harshen kasar Ukraine.

A baya Mykola Yuriychuk ya yi aiki a ramukan hakar ma'adinai a Jezkazgan, Kazakhstan, amma bayan samun nakasu a 1964 ya koma gida zuwa birnin Bukovinian Vashkivtsi . [1] A gida Yuriychuk ya rubuta waƙoƙi don gaba ba tare da wani tsammanin akan abun da zai faru ba kuma ya ba wa abokinsa Mykhailyuk su kamar waɗanda waɗancan waƙoƙin za su yi amfani wata rana. [1] An ajiye rubutacciyar waƙar a cikin akwati kuma an bar su a wurin har tsawon shekara, a cikin shekarar 1965 yayinda yake yawo a cikin lambu, Mykhailyuk ya samar da kidan wakar. [1] Ya ruga zuwa gidansa, ya zauna a piano ɗinsa, ya buga waƙa, sannan ya rubuta rubutu da sauri a kan takarda. [1]

Vasyl Mykhailyuk ya ambata cewa a cikin 1965 shi da ƙungiyar mawaƙa sun yi tafiya zuwa Kyiv don bikin cika shekaru 25 na hadewar Arewacin Bukovina da kasar Ukraine kuma a can Dmytro Hnatiuk ya ji waƙar. [1] Ya ba wa waƙar fikafikai kuma yana mai godiya a gare shi da yasa waƙar ta ratsa duk fadin duniya. [1]

Daga cikin sauran wadanda suka taka rawa akwai Sofia Rotaru, Taisia Povaliy ( Ukraine ), Kvitka Cisyk ( Amurka ), Stepan Pasicznyk ( UK ), Evdokimov Yaroslav Alexandrovich ( Rasha ), Tatiana Bulanova, Aleksandr Malinin ( Rasha ) da sauransu da yawa.[2]

An shigar da waƙar a cikin kundin Kvitka Cisyk Launuka Biyu .

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]