Cherif Mohamed Aly Aidara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cherif Mohamed Aly Aidara
Rayuwa
Haihuwa Darou Hidjiratou (en) Fassara, 1959 (64/65 shekaru)
ƙasa Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a shugaban addini
Imani
Addini Shi'a
Cherif Mohamed Aly Aidara (Institut Mozdahir International)

An haifi Cherif Mohamed Aly Aidara a shekarar miladiyya shekarar 1959 a garin Darou Hidjiratou (Dar Al Hijra). Ɗa ne awajen Maimouna Diao ('yace ga Saydou Diao wanda shima sarki ne) da kuma Cherif Al-Hassane Aidara, daga kasar Mauritania, na kabilar “Laghlal” (wanda aka fi sani da Ahlou Cherif Lakhal). Magabatan sa ta layin Cherif Moulaye Idriss, wanda ya kafa daular Idrissid, wanda jinin Hassan ɗan Ali da Fatima yar Annabi Muhammad (Aminci ya tabbata a gareshi).

Dan kasa biyu ne, Senegal da Muritaniya.

Cherif ya iya magana, karantu da kuma rubutu da harsuna da dama aciki harda Faransanci, Turanci, Larabci, Wolof da kuma Fulatanci.

Rayuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

Cherif Mohamed Aly Aidara

Cherif shine shugaban al'umman Shia Mozdahir na Afirka da duniya baki daya.

Shi ne Kuma shugaba wanda ya kafa Mozdahir International Insitute (NGO).

Shi ne babban shugaban gidan Radiyon Mozdahir FM da Radiyon Zahra FM na garin Dakar da Kolda yadda yake a jere.

Rubutu da yayi[gyara sashe | gyara masomin]

Cherif Mohamed Aly Aidara

Ya rubuta littattafai akan tauhidin musulunci, tarihin annabi Muhammad (tsira da amincin Allah ya tabbata akanshi) da kuma sahabbai 12 da wasu littattafan, harda:

  • Gaskiyar magana akan gadon annabi (Les Vérités de La Succession du Prophète)
  • Sayyeda Zaynab (aminci ya tabbata a gareta), gwarzuwan Karbala (Sayyidda Zaynab (paix et salut sur elle) l'héroïne de Karbala)
  • Sallolin annabi Muhammad (aminci ya tabbata a gareshi) daka bakin iyalan gidan sa (La prière du Prophète Mouhammad (PSLF) selon les membres de sa famille)
  • Ghadir Khum
  • Ashura: Ranar jimami ko ranar murna? (Achoura jour de deuil ou jour de fête ?)
  • Dokokin harkar kudi na musulunci (Principes de la finance islamique)

Duba sauran wasu abubuwan[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]