Francisco Gonçes Sacalumbo (An haife shi a ranar 17 ga watan Disamba 1998), wanda aka fi sani da Chico Banza, ko kuma a sauƙaƙe Chico, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ga kungiyar kwallon kafa ta Nea Salamina.[1]
Kungiyar Leixões ta Portugal ce ta dauko Chico Banza daga kasarsa ta Real Sambila, sakamakon wasan da ya yi a gasar Toulon ta shekarar 2017. Bayan ya taka leda a Club's 'B' ta kulob din a cikin rukunin 'yan wasan Portugal, an sanya shi a wasansa na farko a ranar 18 ga watan Maris 2018, ya buga mintuna 68 a wasan da suka tashi 1-1 da kungiyar kwallon kafa ta Sporting CP B kafin Ricardo Barros ya maye gurbinsa.[2]
Chico Banza ya wakilci Angola a gasar Toulon 2017, inda ya kare a matsayin daya daga cikin manyan 'yan wasan da suka zira kwallaye hudu a wasanni uku. [3]