Jump to content

Chinwe Ohajuruka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Chinwe Ohajuruka
Rayuwa
Haihuwa 1960 (63/64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a Masanin gine-gine da zane
Kyaututtuka

Chinwe Ohajuruka ta kasan ce babbar mai zane ce a Nijeriya.[1][2] Tana raba lokacinta tsakanin Najeriya da Amurka domin yin ayyuka.[3] Ta zama mai wakiltan Afirka ta Kudu da Sahara don karbar Kyautar Mata na Cartier a Faransa a shekarar 2015, saboda gudummawar da ta bayar a hada korayen gidaje masu saukin kudi da kuma zamantakewar kasuwanci.[4]

Ohajuruka itace Shugabar masu zane, Sustainability Consultant da kuma furojet Manager for Comprehensive Design Services, kamfani ne da ke tsarawa da kuma gina gidaje masu amfani da hasken rana; kamfanin da ta kafa a 2012.[5][6] Kamfanin nata yana samar da gidaje ta amfani da wata dabara da ake kira Bio-Climatic Design, wanda ke amfani da dabarun ƙira da dabarun aikin injiniya waɗanda suka dace da yanayin yankin, da kuma haɗa rijiyoyi masu amfani da hasken rana. Ta koma Amurka daga Najeriya a 2003.

Lamban girma

[gyara sashe | gyara masomin]

An nada Ohajuruka a matsayin "Babbar Mai Kalubalantar Makamashi da turanci Great Energy Challenge Innovator" kuma an ba ta tallafi daga National Geographic don aikinta a Port Harcourt, Najeriya, Gidaje masu araha tare da sabunta makamashi ga Najeriya . Ta kuma sami lambar yabo ta Kimiyya da Fasaha daga Gidauniyar Chenving. An ba ta lambar yabo ta Injiniyar Mata ta Cartier.[7] Kamfanin ta kuma ya samu tallafi daga USAID da kuma Western Union Foundation.[8][9][10]

  1. https://africa.com/the-african-diaspora-beyond-remittance/
  2. https://www.independent.ng/the-world-is-waiting-for-the-rise-of-african-women-ohajuruka/
  3. https://www.cdshousing.com/our-team
  4. http://afrique.lepoint.fr/economie/cartier-women-s-initiative-awards-2015-l-afrique-renouvelle-son-double-19-11-2015-1983087_2258.php
  5. https://www.chevening.org/cheveners/science-and-technology/
  6. https://www.straitstimes.com/world/africa/moving-nigerians-from-slums-to-their-own-green-homes
  7. "Cartier Womens Initiative Awards" (PDF). Retrieved 9 March 2020.[permanent dead link]
  8. https://www.csmonitor.com/World/Africa/2018/0614/One-company-s-plan-to-create-affordable-green-housing-in-Nigeria
  9. https://www.environewsnigeria.com/affordable-green-housing-designer-may-decorated/
  10. https://www.nawbo.org/sites/default/files/Cartier-2016-Brochure.pdf[permanent dead link]