Jump to content

Chris Aire

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Chris Aire
Rayuwa
Haihuwa 25 Disamba 1964 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta California State University, Long Beach (en) Fassara
Sana'a
Sana'a jeweler (en) Fassara

Christopher Aire (an haife shi ranar 25 ga watan Disamban shekarar 1964) ɗan Najeriya-Amurika ne, mai saida kayan ado kuma mai zane ko tsara fasalin agogo.[1] Shi ne shugaban kamfanin Solid 21 Incorporated kuma wanda ya kafa tambarin sa mai suna Chris Aire.

Shekarun farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Chris Aire a Ivue-Uromi, Najeriya .[1] Mahaifinsa Joseph Agimenlen Iluobe dan Najeriya ne kuma ɗan kasuwa[1] mahaifiyarsa itace, Victoria Isesele Iluobe. Yayi karatu a Immaculate Conception College, Benin City, Najeriya. Bayan haka, mahaifinsa ya so ya shiga kasuwanci. Aire ya fara taimaka wa mahaifinsa wajen gudanar da kasuwancin jigilar mai, amma ya gane cewa yana da sha'awar yin aiki da kansa na ƙashin kansa. Bayan ya yi aiki na ɗan lokaci a kamfanin mahaifinsa Iluobe Oil, ya yanke shawarar barin Najeriya ya koma Amurka don ci gaba da karatunsa kuma ya halarci Jami'ar California State University Long Beach. Yayin da yake makarantar koleji, Aire ya yi ayyuka marasa ƙarfi a gidajen cin abinci. Ya kammala karatunsa na digiri a fannin wasan kwaikwayo da kuma bayar da umarni.[2]

Ƴa fara wasan kwaikwayo da ƙafar haggu-( bai yi nasara ba), don haka Aire ya yanke shawarar gwada basirarsa a fannin kiɗa. Ya shiga ƙungiyar da ake kira Raw Silk, tare da haɗin gwiwa da yin aiki tare da ƙungiyar na ɗan wasu shekaru. Ƙungiyar ba ta fuskanci irin nasarar da ya yi fatan samu ba, don haka ya sauya shawara.[2]

Daga baya, Ya karɓi aiki a matsayin mai koyo, ga wani mai kayan ado a Los Angeles, California, mai suna P-5 Jewelers.[1] Ba da da ewa bayan, ya shiga a Gemological Institute of America, Carlsbad inda ya karbi diamond-grading diploma.[ana buƙatar hujja]

A cikin 1996, bayan shekaru shida na koyo tare da wani mai suna P-5 Jewelers, ya tashi da kafafunsa-(ya zama ubangidan kansa). Ya tanadi dala 5,000 don fara tambarin sunan kamfaninsa na ƙira da siyar da kayan ado da agogo masu kyau.

Ba da daɗewa ba bayan kafa Chris Aire, ya haɗu da Gary Payton, babban tauraron NBA wanda a lokacin yana tare da ƙungiyar ƙwallon kwando ta Seattle SuperSonics. Payton ya nuna sha'awar zanensa kuma ya gayyaci Aire ya same shi a Miami a wani taron bada tallafi a wata mai zuwa. A Miami, ya sami tsari mai mahimmanci, yana ƙarfafa matsayinsa a cikin kasuwar kayan ado.[2][3]

Aire ya buɗe Boutique-(kantin siyar da kayan sawa) dinsa na farko[4] a otal din Transcorp Hilton dake Abuja, Najeriya, a shekarar 2012. A cikin 2014, Aire ya koma ofishinsa na Amurka daga cikin garin Los Angeles zuwa otal ɗin tutar Amurka a Beverly Hills.[5]

Recognition and titles

[gyara sashe | gyara masomin]

Jaridar Los Angeles Times ta bayyana Air a matsayin "Sarkin Bling".[6] Mujallar Rolling Stone ta kira shi da "The Emperor of Ice".[4] An nuna Aire a cikin wasu mujallu da yawa kamar Forbes,[7] Wall Street Journal, IDEX[8] JCK MAGAZINE,[9] Elle, Vogue, Black Enterprise,[10] Robb Report,[11] Watch time, Mujallar QP,[12] Mujallar Rapaport,[13] da Mujallar Los Angeles.[14]

An kuma nuna shi a CNN,[6] Konnect Africa,[15] Washington Times,,[16] USA Today,[17] da kuma Discovery Channel.[18]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Aire ya auri Diana Atinuke Durojaiye. Suna da 'ya'ya uku. Yana zaune a birnin Los Angeles kuma sau da dama ya kan ziyarci Najeriya a wasu lokutan.

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Nsehe, Mfonobong. "Meet Chris Aire, The King of Bling And Jeweler To Hollywood's Elite". Forbes (in Turanci). Retrieved 2022-02-28.
  2. 2.0 2.1 2.2 "CHRIS AIRE: A Nigerian can succeed anywhere in the World". Vanguard News (in Turanci). 2013-03-10. Retrieved 2022-02-28.
  3. Vladimir Duthiers. "How Chris Aire hustled his way to become Hollywood's 'King of Bling'". CNN (in Turanci). Retrieved 2022-02-28.
  4. 4.0 4.1 "Chris Aire Will Open First Retail Boutique". Instoremag.Com. Retrieved 2015-09-18.[permanent dead link]
  5. "Chris Aire". Chris Aire. 2014-10-02. Retrieved 2015-09-18.
  6. 6.0 6.1 "How Chris Aire hustled his way to become Hollywood's 'King of Bling'". CNN.com. Retrieved 2015-09-18.
  7. "Meet Chris Aire, The King of Bling And Jeweler To Hollywood's Elite". Forbes.com. Retrieved 2015-09-18.
  8. "IDEX Magazine - Full Story". Idexonline.com. 2005-09-05. Archived from the original on 2015-09-29. Retrieved 2015-09-18.
  9. George, William. "A Jeweled Watch Movement - JCK". Jckonline.com. Archived from the original on 2016-03-15. Retrieved 2015-09-18.
  10. "Chris Aire". Connection.ebscohost.com. 2006-04-06. Archived from the original on 2015-09-28. Retrieved 2015-09-18.
  11. Francis Addo (2011-12-19). "Ghanaian Actress Caught With Chris Aire ~". Ghanashowbiz.blogspot.com. Retrieved 2015-09-18.
  12. "King of Bling" (PDF). Qp.granularit.com. Archived from the original (PDF) on 2015-09-29. Retrieved 2015-09-27.
  13. "Chris Aire Hits the Runway With $175 Million of Diamonds". Diamonds.net. Retrieved 2015-09-18.
  14. Los Angeles Magazine. June 2002. p. 70. Retrieved 2015-09-18 – via Internet Archive. Los Angeles magazine rock stars chris aire.
  15. "Chris Aire, The King Of Bling!!!". Konnectafrica.net. 2013-03-20. Retrieved 2015-09-18.
  16. "Ice, ice baby". Washington Times. Retrieved 2015-09-18.
  17. Carter, Kelly (2003-01-17). "USATODAY.com - To celebrities, Aire is a gem". Usatoday30.usatoday.com. Retrieved 2015-09-18.
  18. "Diamond Road (Documentary) - Trailer (2008)". YouTube. 2007-07-24. Retrieved 2015-09-18.