Ciwon huhun daji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
alamun Ciwon daji a nono

Ciwon huhun daji ciwo ne qari huhu ana danganta shi da girmar tantani mara magani na fale-falen nama ta huhu. Idan ba a nemo magani ba, wannan girmar zata yadu nisa da huhun ta hanyar metastasis zuwa fale-falen nama ko sassan jikin. Yawancin ciwon daji da ke faruwa a huhu ana ce da su ciwon huhun daji na farko, acrcinomas. Ainihi waxannan ire-ire biyu sune; karamin-tantanin huhun carcinoma (SCLC) da mara-karamin-tantanin huhun carcinoma (NSCLC). Yawan alamomin wannan ciwo sune; tari (da tarin jini), ramewa, kasawar nufamshi da ciwon kirji.

Qato bisa xarin jama'a tamanin da biyar (85%) na matsalolin ciwon huhun daji ya nuna cewa shan tava na tsawon lokaci na kawo ciwon. Sa'annan 10-15 bisa xari (10-15%) matsalolin wannan ciwo ya samu ne ta rashin shan tava/sigari. Waxannan matsalolin na sa haxuwa matsalar kayyade da watsawa zuwa rado gas, asbestos, da wasu hayakin kone-kone da wasu gurvacewar iska. Za a iya ganin ciwon huhun daji kamar ciwon kirji ne idan an yi hoto aka kuma hada duba da na'ura (CT). Gwajin ta bayyanu ta bayosfsi wanda kullum ana yinta bronchoscopy ko na'ura mai kwakwalwa.

Rigakafin shi ne ta kiyaye haxarin kamuwa da ita, tare da shan hayaki da kuma gurvacewar iska. kula da wannan da sakamako na tsawon lokaci ya danganta ga irin ciwon huhun dajin, yanayinta (yadda ya ke yaxuwa), da kuma dukan lafiyar mutumin. 'yawancin matsalolin ba a iya magance su. Maganinsa na yau dakullum ya hada da fixa, da magangunan kimiya, da dauka hoton. Ana iya magance NSCLC da fixa wasu lokuta, sa'annan SCLC kuma qan ji magangunan kimiya da daukan hoton da sauri fiye da fixa.

File:Clatterbridge Cancer Centre, Liverpool . 2.jpg
Babban Asibitin kula da Ciwon daji dake Liverpool

A duniya gaba xaya a shekara ta 2012, an same mutum miliyan xaya da digo takwas (1.8 million) an gwada su da ciwon huhun daji, sa'anan mutum miliyan xaya da digo shida sun mutu da dalilin ciwon (1.6 million). Wannan ya zamma sanadiyyar mutuwa a maza na ciwon huhun daji gama gari da ya faru da na biyu cikin sanadiyyar mutuwar mata bayan ciwon-nono. 'yan shekaru saba'in ne an fi gwada su da wannan cutar. Mutane kashi sha bakwai da digo hudu cikin xari cikin Qasar Amurka an gwada su da wannan ciwon huhun daji, sun rayu da ciwon na shekaru biyar bayan gwajin, sa'anan sakamakon a Qaddarance a Qasashe masu tasowa.