Dachung Musa Bagos

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dachung Musa Bagos
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
Dachung Musa Bagos
District: Jos South/Jos East
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023
Kaze Bitrus - Dachung Musa Bagos
District: Jos South/Jos East
Rayuwa
Haihuwa 4 ga Yuni, 1977 (46 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

An haifi Dachung Musa Bagos a ranar 4 ga watan Yunin 1977 a Apata, karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato dan siyasar Najeriya ne daga jihar Filato a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party.[1] Shi dan Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ne daga mazabar Jos ta Kudu / Jos ta Gabas na Jihar Filato a Majalisar Tarayya ta Tara. An zabe shi a majalisan a 2019.[2][3][4]

Ya fara neman ilimi ne a makarantar firamare ta Ekan, daga nan kuma ya wuce makarantar Jos Development Enterprise Commercial inda ya samu digirin sa na uku kuma ya samu shaidar difloma a Secretariat Administration.[5] Dachung ya wuce Jami'ar Jos inda ya sami Difloma a fannin Shari'a, daga nan kuma ya sami Makarantar Jos ECWA Theological Seminary don faɗaɗa iliminsa da fasaharsa.[6]

Rayuwa ta sirri da taimakon jama'a[gyara sashe | gyara masomin]

Domin inganta ilimin mazabar sa, Honorabul Dachung Musa Bagos ya kaddamar da ajujuwa na zamani guda biyu masu dauke da ofisoshi da shaguna da kuma nau'ra mai amfani da hasken rana ga daliban makarantar firamare ta Gwandang LEA dake Bukuru-Gyel dake karamar hukumar Jos ta kudu ta jihar Filato.[7] Ya kuma biya wa dalibai mata na Government Technical College Bukuru kudaden makaranta tare da raba daruruwan litattafan motsa jiki ga daliban makarantar.[8] Gidauniyar Dachung Musa Bagos ta bayar da tallafin karatu ga dalibai 598 na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Godong dake karamar hukumar Jos ta Gabas, da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Chugwi dake karamar hukumar Jos ta kudu.[9]

Bayan wani hari da 'yan ta'addan Fulani suka kai a jihar Filato a ranar Lahadi 31 ga watan Yuli, inda aka kashe kiristoci bakwai tare da raunata wasu biyu, Bagos ya ziyarci wadanda abin ya shafa, inda ya yi Allah wadai da kashe-kashen da suka yi da cewa “abin kunya ne” da kuma “rauta”, tare da biyan kudaden jinya ga wadanda suka jikkata.[10]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Jam'iyyar PDP

Jihar Filato

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "National Assembly Federal Republic of Nigeria]". www.nass.gov.ng (in Turanci). Retrieved 2021-07-16.
  2. "Dachung Bagos Makes it to Reps]". orderpaper.ng (in Turanci). 22 April 2019. Archived from the original on 2021-07-13. Retrieved 2021-07-14.
  3. "Nigerian House of Representatives, Members of House of Representatives in Nigeria :: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2021-03-05.
  4. "Nigerian House of Representatives, Chairmen and deputies of Standing and special committees, House of Representatives in Nigeria ::". www.placng.org. Retrieved 2021-03-05.[permanent dead link]
  5. "Dachung Musa Bagos]". www.sunnewsonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-07-14.
  6. "Dachung Bagos Profile]". www.accountablenigeria.org (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-13. Retrieved 2021-07-14.
  7. "Lawmaker Commissions 2 Modern Classrooms In Jos South".
  8. "Plateau House of Rep. Member, Hon. Bagos Dachung Pays School Fees for All Female Students of BUTECH, Distributes Books to Students". 21 March 2020. Archived from the original on 8 December 2022. Retrieved 8 December 2022.
  9. "Bagos Presentation of Scholarship]". www.thestateofplateau.com (in Turanci). Retrieved 2021-07-14.[permanent dead link]
  10. "Seven Christians killed in Islamist attack in Plateau State, Nigeria". barnabasfund.org (in Turanci). Retrieved 2022-08-28.