Daisy W. Okocho

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Daisy W. Okocho
Rayuwa
Haihuwa Obio-Akpor, 15 ga Janairu, 1951 (73 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a mai shari'a

Daisy Wotube Okocha (an haife ta 15 Janairu 1951) itace babbar mai Shari'a a jihar Ribas ta 17.[1] Gwamna Ezenwo Wike ne ya naɗa ta a a ranar 4 Janairu 2016,[2] ta riƙe muƙamin har 15 Janairu 2016.[3] Da farko ta fara zama muƙaddashiyar kafin ta zama cikakkiyar mai Shari'a daga bisani.[4][5]

Farkon rayuwa da ilmin[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Okocha ranar 15 ga Janairu 1951 a Obio-Akpor, jihar Rivers, Najeriya. Ita ƴar ƙabilar Ikwerre ce. Mahaifin ta Jonathan Okocha, tsohon Kwamishina ƴan sanda ne, mahaifiyar ta Helen Nonyelum Okocha, Mai kulawa ce.[6]

Daisy tayi karatun digiri ne a jami'ar Ahmadu Bello Zariya a 1978. A shekarar 1979 ta zama cikakkiyar lauya.[7]

Aikin Shari'a[gyara sashe | gyara masomin]

A 1981, Okocha ta shiga ma'aikatar Shari'a ta jihar Ribas. Ta sha samun ƙarin girma da dama. A 1991, ta zama babbar mai Shari'a a jihar Ribas inda tayi aiki a Fatakwal.[7]

Ta maye gurbin Iche Ndu a matsayin muƙaddashiyar mai Shari'a a 2013. Da farko gwamna Chibuike Amaechi ya ki tabbatar da ita.[8] A Yuni 2015, ƙarƙashin jagoraci gwamnatin Ezenwo Wike, Okocha tasha rantsuwa ta kama aiki a matsayin babbar mai Shari'a ta jihar Ribas. Itace mace ta farko da ta fara hawa wannan muƙamin.[9]

Okocha ta taɓa rike matsayin ma'ajiya a ƙungiyar mata alƙalai ta Najeriya da kuma wasu muƙamai a ƙungiyoyi na gida dama na waje.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Chioma, Unini (2016-01-05). "Rivers gets first female chief judge". TheNigeriaLawyer (in Turanci). Retrieved 2020-05-28.
  2. Ihunwo, Tony (2016-01-04). "Governor Wike Swears In First Female Chief Judge In Rivers State, What She Said (PHOTOS)". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2020-05-28.
  3. Amadi, Akujobi. "As Justice Okocha Bids Rivers Judiciary Farewell" (in Turanci). Retrieved 2020-05-28.
  4. "Daisy Okocha Takes Oath As Substantive CJ". The Tide. 4 January 2016. Retrieved 11 February 2016.
  5. Akujobi Amadi (20 January 2016). "As Justice Okocha Bids Rivers Judiciary Farewell". The Tide. Retrieved 11 February 2016.
  6. Chioma, Unini (2016-01-05). "Rivers gets first female chief judge". TheNigeriaLawyer (in Turanci). Retrieved 2020-05-28.
  7. 7.0 7.1 7.2 "Justice Daisy Okocha". Rivers State Judiciary. Archived from the original on 19 September 2014. Retrieved 3 June 2015.
  8. Onukwugha, Anayo (3 October 2014). "I Hold Nothing Against Okocha – Amaechi". Leadership. Archived from the original on 29 November 2014. Retrieved 3 June 2015.
  9. "Rivers Names Female CJ …As Iche Ndu Retires Next Month". The Tide. 29 July 2013. Retrieved 3 June 2015.