Jump to content

Daura

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Daura


Wuri
Map
 13°02′11″N 8°19′04″E / 13.0364°N 8.3178°E / 13.0364; 8.3178
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
Ƙaramar hukuma a NijeriyaDaura (en) Fassara
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 474 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
dan makaranta a GDSS Daura
Ƙofar sarki Musa
Bayajidda primary school Daura
Masallacin GRA Daura
Babbar kasuwar Daura
Daura wata karamar hukumace a jarar katsina
Daura_Court

Daura wata karamar hukuma ce wacce take a cikin jihar Katsina, a Arewacin Najeriya. Masarautar Daura ta hada da wasu kananan hukumomi da suke kewaye da ita wadanda suka hada da Daura, Baure, Zango, Sandamu, D

utse, Mai'aduwa da kuma ita Daurar. Daura ta yi iyaka da Nijar kuma tana daya daga cikin garuruwan Hausa bakwai, wadanda suka hada da Gobir, Biram, Katsina, Kano, Zazzau da Rano, wanda 'ya'yan Bayajidda da jikokin shi suka mulka.

Tarihin Daura ya fara ne daga lokacin da wasu mutane daga garin Daura wanda take garin Katsina a yanzu markashin jagorancin wani Namangi, ya kasance mutum ne mai daraja wanda ya taba shan kaye a wajen takarar sarautar Daura. Ya kuma yanke shawara ya koma da zama a wani karamin gari kusa da karaye, wanda ake kira kardozama.[1] Ya kasance yana zuwa bakin wani kogi a cikin garin inda ya gano cewa lallai wajen zai yi dadin zama.Ya samu fili a wajen kuma ya gina gida. Zai huta a gidan na wasu lokuta Sannan ya wuce karaye. A haka ne har aka far kiran wajen da suna Daurawa. Wannan shine asalin tarihin kauyen Daura.[1] Garin baida katanga da ta zagaye shi, saboda tayi kusa da karaye sosai, kuma duk lokacin da za a kuma buga tambarin sarauta, mutanen cikin garin Daura zasu garzayo cikin karaye saboda su samu tsaro. [1]

Ta hada iyaka da magajin gari da taurawa kafin ginin challawa gorge Dam, kauyen yola, kauyen ma, da kuma magajin hajj ta kudu, yamma, gabas da kuma arewa.

Ƙauyen Daura ya gunshi Gundumomi guda shida:

1-    Daura Cikin Gari

2-    Daura Mai Ruwa

3-    Gatarawa

4-    Alfawa

5-    Kwari

6- Daura Saƙo[1]

  • G. Karaye, Ibrahim, J. Philip, Shae. History of karaye. ISBN 978-125-341
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 G. Karaye, Ibrahim, J. Philip, Shae. History of karaye. p.p 168-169 ISBN 978-125-341

Samfuri:Kananan Hukumomin Jihar Katsina