Doka ta rashin adalci ba doka bace ko kadan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Doka ta rashin adalci ba doka bace ko kadan
saying (en) Fassara

Doka ta rashin adalci ba doka ba ce ko kadan, a harshen Latin lex iniusta non est lex, furci ne doka na zahiri, wanda ke nunan cewa hukunci ba ta zama halaltacciya face idan tana da kyau kuma an tsarata akan hanyar da ta dace. Ta zama doka ta gama gari ta maxim a duniya. [1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

A tarihance, marubutan falsafa da na addini sau da yawa suna adawa da dokoki na rashin adalci. Misali, a cikin Ishaya 10 :

Bone ya tabbata ga wadanda suke kirkirar rashin adalci acikin mulki,

ga waɗanda ke bada dokoki na muzgunawa,
don tauyewa talakawa hakkinsu

da kuma rashin hukunta masu laifi ga jama'ata

A karni na huɗu AD, Augustine na Hippo[2] ya ce "a tunani na doka wacce ba ta adalci ba ce, a zahiri doka bace" (" nam mihi lex esse non videtur, quae justa non fuerit "). [3] Ya rubuta wannan sa’ad da yake magana game da dalilin da ya sa mugunta ke wanzuwa. Ya karkare da cewa a ƙarshe matsala ce da mutane ke barin hali mai kyau ko adalci. Ya kamata a bi dokoki? Haka ne, amma idan sun kasance masu adalci.

Thomas Aquinas [4] ya yi nazari sosai kan ingancin dokokin da dan-adam ke tsarawa sannan kuma ko ya kamata a yi musu biyayya, a cikin littafinsa na Summa Theologica. Ya tambaya "Shin dole ne a bi dokokin da mutum ya yi?" Amsar sa ita ce a'a; doka tana buƙatar a bi ta ne kawai idan ta halalta ta hanyoyi uku:

  1. Manufa: Dole ne doka ta kasance don amfanin jama'a.
  2. Marubuci: Dole ne ya kasance a cikin iyakokin ikon yin doka.
  3. Sifar doka: Kuma nauyinsa ya zama daidai kuma ya shafi kowa.

Aquinas ya ce bai kamata ace rashin biyayya kadai ta jawo lahani ba ko kuma ya kai mutane cikin mugunta. Ya yi nuni ga littafin Ishaya wanda ya nuna cewa ya halatta a guje wa zalunci koyaushe.

A cikin Rashin Biyayyar 'yan kasa (Civil Disobedience), Henry David Thoreau ya kuma yi zargin sahihancin duk wata doka da ta kasance ta adalci. Yana cewa:

“Akwai dokoki na rashin adalci:
shin zamu zamo masu biyayya a garesu,
ko kuwa zamu agaza wajen gyara su,
sannan mu cigaba da bin su har sai munyi nasara,
ko kuwa zamu butulce masu ne tun yanzu?”

Martin Luther King Jr,[5] a cikin wata wasikarsa daga gidan yari na Birmingham, yayi magana akan duka Augustine da Aquinas, yana mai cewa dokokin Jim Crow ba na adalci bane kuma ya kamata a kauce musu, wajen kafa dalilinsa na alherin rashin bin daka na jama'a.

Indiya[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin falsafar kasar Indiya, ra'ayin cewa doka ba ta cika doka har sai ta cike ra'ayoyin Ṛita, watakila tana nufin ''hakkoki" da Hausa. Wannan dokoki na asali sun kafa ƙa'idojin na abinda ake kira "doka" ko kuma "gaskiya", wasu irin ka'idoji madaukaka wanda ko Allolinsu sai sunyi biyayya ga su ko kuma su saba. Wdannan dokoki basu jagorar addinin Ritanci, amma suna a matsayin hukunce-hukunce kuma wakilai.[6]

Wannan doka tana da alaka da masana dokokin asali irinsu John Finnis da kuma Lon L. Fuller.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://lawtutor.co.uk/lex-iniusta-non-est-lex
  2. The Encyclopedia of language and linguistics, Volume 4
  3. St. Augustine, De libero arbitrio voluntatis, b. 1, s. 5., 1.5.11.33
  4. Norman Kretzmann, Lex Iniusta Non Est Lex: Laws on Trial in Aquinas' Court of Conscience, 33 Am. J. Juris. 99 (1988). Thomas Aquinas, Summa Theologiae I-II, q. 96, a. 4, c.
  5. "Letter from a Birmingham Jail [King, Jr.]". www.africa.upenn.edu.
  6. Day (1982:29–30).
  7. Brian Bix, "Jurisprudence: Theory and Context", (Sweet&Maxwell 2009) 70