Dunama IX Lefiami

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dunama IX Lefiami
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a

Dunama Lefiami shi ne Sarkin daular Kanem-Bornu, wacce take a yanzu a yankin Najeriya, Kamaru da Chadi a farkon karni na sha tara.

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Dunama ya gaji mahaifinsa, ya kasance tsoho kuma ya makance, shine wanda ya jajirce a cikin Jihadin Fulani har ya sa aka kama Ngazargamu . Mai Dunama ya nemi goyon bayan Muhammad al-Amin al-Kanemi, don su taimaki Fulani a yaki na gaba da gaba, ya amsa kiransa, Bayan angama yaki Dunama ya bashi Bayi da kayan masarufi, bayan anci Goni Mukhtar da yaki. a shekarar 1809 an sake karbar Ngazarmu, manyan mutanen sun tilasta Dunama da ya gudu, sai aka nada kawunsa a matsayin sarki Muhammad Ngileruma Mai. A 1813 yan fada sun gaji da Ngileruma, sai suka dawo da Dunama a matsayin Mai, amman duk da haka saida aka kashe Dunama a yaki bayan ya jagoranci yakin tawaye ga masarautar el-Kanemi a 1819 ko 1820 [1]

Diddigin bayanai[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Herbert Richmond Palmer, The Bornu Sahara and Sudan (London: John Murray, 1936), pp. 95,259-268.