Jump to content

Emem Isong

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Emem Isong
Rayuwa
Cikakken suna Emem Isong
Haihuwa 20 century
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Calabar
Federal Government Girls College, Calabar (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a mai tsara fim, marubin wasannin kwaykwayo da darakta
Imani
Addini Katolika
IMDb nm2130579
youtube.com…
hoton emem isong

Emem Isong na ɗaya daga cikin mata wadanda suka soma gudanar da harkar fina-finan 'yan kudu wadanda ake kiran masana'antarsu da Nollywood. Ta kwashe sama da shekaru 25 tana kare 'yancin mata a cikin masa'antar ta Nollywood. Ta shiga gasanni daban-daban ta kuma yi zarra inda ta lashe gasa daban-daban kama daga na cikin gida da na kasashen waje. A shekarar 2018 ta lashe gasar "African Film Leadership Award" a wajen wata gasa da aka shirya wa masu harkar fim na Afirka, wadda aka yi a Dallas ta kasar Amurka. Ta kuma lashe wadansu kyaututtukan a cikin wadansu gasannin da aka shirya a Afirka wadanda suka hada da "Giama Award" da "Thema Award" da "ZAFAA Award" da "Best Nollywood Award" da "City People Awards" da kuma "AMAA Awards" (gasar da ake yi a Afirka wadda ta yi kama da ta Oscar).