Emmanuel Ogalla
Appearance
Emmanuel Ogalla | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Rear Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla (an haife shi a ranar 20 ga watan Disamba shekarar ta alif dari da sittin da takwas (1968) babban hafsan sojojin ruwa ne a Najeriya wanda shine babban hafsan sojojin ruwa na Najeriya. Shugaba Bola Tinubu ne ya nada shi ranar 19 ga watan Yuni shekarar 2023.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Emmanuel Ikechukwu Ogalla a ranar 20 ga watan Disamba shekarar 1968 daga jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya. Ya samu takardar shedar Makaranta ta Yammacin Afirka a Makarantar Soja ta Najeriya, Zariya a shekarar 1987. Ya samu digiri na biyu (BSc) a fannin lissafi da kuma MSc a fannin dabarun nazari a jami'ar Ibadan .