Eniola Abioro
Eniola Abioro (An haife ta ne a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara wato 1999). 'Yar Najeriya ce kuma Ita ce samfurin mace a Najeriya ta farko da ta yi tafiya zuwa Prada na kasar Italy . [1]
Rayuwa ta farko
[gyara sashe | gyara masomin]Abioro ita ce ta tsakiya a cikin iyalinta; tana da ɗan'uwa da ƙanwarta.[2] Ta yi aiki a matsayin malamar makarantar sakandare a makarantar da ake kira Grace Academy a garin Legas da ke kasar Najeriya . Wani mai mallakar hukumar gida ya gano ta kuma ya shawo kan iyalinta su bar ta ci gaba da aikin modelin wato ado don jama'a su gani su yaba a cikin samfurin.[3]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Abioro ya sanya hannu tare da Next Management kuma ya fara aiki a matsayin Prada na musamman a cikin shekara dubu biyu da goma sha takwas wato 2018.[3] Ta yi tafiya a kan titin Versace, Giambattista Valli, Tommy Hilfiger, Off-White, Miu Miu, Saint Laurent, Paco Rabanne da Loewe, Salvatore Ferragamo da Altuzarra . [4] Ta kuma yi tafiya ga Jason Wu kuma ta yi aikin modelin kokuma samfurin a kamfanin Revlon, Fenty Beauty, Calvin Klein da Tiffany da Co.[5] Bayan kakar wasa ta farko, models.com ta lissafa ita Abioro a matsayin "Top Newcomer", wato babbar sabuwar zuwa kuma a matsayin daya daga cikin "Top 50".[6][7]
Abioro ta bayyana a cikin editoci na Vogue, Harper's Bazaar, Vogue Italiya, WSJ da Elle.[5]
Bayanan da aka ambata
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Agbo, Njideka (23 February 2018). "ENIOLA ABIORO BECOMES FIRST NIGERIAN TO WALK FOR PRADA". Guardian Nigeria.
- ↑ "Daily Duo: Eniola". models.com. 6 September 2017.
- ↑ 3.0 3.1 Okwodu, Janelle (3 April 2018). "This Nigerian Stunner Taught Kindergarten—Now She Rules the Runways". Vogue. Condé Nast. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "voguejo" defined multiple times with different content - ↑ Adams, Brittany (13 March 2018). "18 NEW TOP MODELS WHO HAD THE BIGGEST FALL 2018 BREAKOUT SEASONS". Fashionista.com.
- ↑ 5.0 5.1 Ojo-Felix, Irene (19 November 2020). "The Graduates: Eniola Abioro". models.com. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "grads" defined multiple times with different content - ↑ Moskovic, Stephen (8 March 2018). "Newcomers F/W 2018".
- ↑ "Top 50 Models". models.com.