Jump to content

Enver İzmaylov

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Enver İzmaylov
Rayuwa
Haihuwa Fergana (en) Fassara, 12 ga Yuni, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Kungiyar Sobiyet
Ukraniya
Karatu
Harsuna Harshan Ukraniya
Sana'a
Sana'a jazz musician (en) Fassara, guitarist (en) Fassara, jazz guitarist (en) Fassara da mai rubuta kiɗa
Kyaututtuka
Artistic movement jazz (en) Fassara
Kayan kida Jita
Enver Izmaylov dan Ukrainian guitar virtuoso ne. 1993
Gasar suturar maƙera a bikin maƙera na duniya karo na 12 a Donetsk

Enver İzmaylov ( Ukraine, Russian: Энвер Измайлов ) an haife shi (12 ga Yuni, 1955) ɗan kabilar Tatar ne na Crimean kuma mawakin jita na jazz wanda ke amfani da salon bugawa Jitan mai amfani da lantarki.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Enver İzmaylov a Fergana, Uzbek Soviet Socialist Republic, Tarayyar Soviet acikin dangin Tatar Crimean da aka kora a baya daga Crimea wanda daga bisani ya sake komowa a 1989.

Duk da cewa yana kada jita tun yana dan shekara goma sha biyar, ya karanci bassoon a Makarantar Kida ta Fergana kuma ya kammala a 1973. Ya kasance memba na ƙungiyar Sato har na tsawon shekaru takwas kuma ya fito a cikin albam din Efsane (1986) da kuma Give Your Love for a Friend in a Circle a (1987). Ya koma makaranta ya sami digiri a Jami'ar Tashkert, sannan ya fara sana'ar solo.[1]

İzmaylov yana kada jita ne ta hanyar kadata ta wuyan gitar lantarki da yatsansa kamar keyboard.[2][3] Salo iri daya daya da ta makadin jita na salon jazz Stanley Jordan.[1]

Enver İzmaylov

İzmaylov yana kiɗan gargajiya na Crimean Tatar, Baturke, Uzbek, Balkan, kiɗan gargajiya, da kuma jazz . Yawancin sassan wakokinsa ana haɗa su cikin salo na lokaci kamar 5/8, 7/8, 9/8, 11/8, 11/16, da 13/16 waɗanda suka zama ruwan dare a salon kiɗan Tatar na Crimean. Yana da jita mai wuya uku wanda ake kera masa na musamman a Kyiv. Yana amfani da sauti guda biyu marasa daidaituwa: (daga ƙanana zuwa manya) E, B, E, E, B, E da C, C, G, C, C, C.[2]

'Yar Enver Leniye İzmaylova shahararriyar mawakiya ce a tsakanin mawakan Tatar Crimean. Ta na kida da salon gargajiya, jazz, da kiɗan pop a cikin wakokinta.

  • A Ferghana Bazaar (Tutu, 1993)
  • Art na Duo tare da Geoff Warren (Tutu, 1996)
  • Labarin Gabas (Boheme, 1998)
  • Minaret (Boheme, 1999)
  1. 1.0 1.1 Harris, Craig. "Enver Izmailov". AllMusic. Retrieved 12 August 2017.
  2. 2.0 2.1 Prasad, Anil (1 July 2010). "Enver Izmaylov". Guitar Player. Retrieved 13 August 2017.
  3. Yanow, Scott (2013). The Great Jazz Guitarists. San Francisco: Backbeat. p. 220. ISBN 978-1-61713-023-6.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]