Fasa gidan yari a Agodi
Iri |
prison escape (en) aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 11 Satumba 2007 |
Wuri | Jahar Oyo |
Ƙasa | Najeriya |
Adadin waɗanda suka rasu | 8 |
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 18 |
Fasa gidan yari na Agodi dai wani hari ne da aka kai a gidan yarin Agodi mafi ƙarancin tsaro da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo a Najeriya, inda wasu masu aikata laifuka suka kai hari. An bayyana cewa; kimanin fursunoni takwas ne suka mutu a yunƙurin tserewa, da wasu goma sha takwas da suka jikkata.[1]
Lamarin
[gyara sashe | gyara masomin]An ruwaito lamarin da ya faru ne a ranar 11 ga watan Satumba, 2007.[2] Wasu gungun masu laifin ne suka shirya hakan, waɗanda aka yankewa hukuncin ɗaurin rai da rai don yunƙurin tserewa daga gidan yarin.[3] Labarin ya fara ne sa’ad da mai kula da kurkukun da ke bakin aiki ya so ya baiwa fursunonin karin kumallo.[4] Nan take aka buɗe kofar suka fice daga cikin dakin da karfi da yaji, inda suka lakaɗawa jami'in duka da ƙoƙarin sakin wasu fursunoni daga cikin dakunan su.[5] Jami’an ƴan sanda sun isa wurin domin daƙile fasa gidan yarin wanda hakan ya haifar da arangama tsakanin fursunonin da ƴan sandan.[6] Hakan ya yi sanadiyar mutuwar fursunoni takwas tare da jikkata wasu goma sha takwas.[7] Yunƙurin tserewar ya ci tura, sakamakon babu wani fursuna da ya iya samun damar tserewa daga gidan yarin.[8]
Mauren Omeli, babban jami’in gidan yarin na jihar Oyo wanda ya tabbatar da harin ya yi ikirarin cewa fursunonin sun yi yunƙurin tserewa ne saboda fargabar rashin isassun kulawar lafiya.[9]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Details - The Nation Archive". Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "Reference at allafrica.com".
- ↑ Independent Newspapers Online. "Failed jail break sees eight inmates killed". Independent Online. Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "Prisoners dead in Nigerian jailbreak". 12 September 2007. Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "Nigerian Prisoners Die in Attempted Jailbreak". VOA. Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "Nigerian Prisons And Incessant Jailbreaks - Nigerian News from Leadership Newspapers". Nigerian News from Leadership Newspapers. Archived from the original on 26 December 2014. Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "Details - The Nation Archive". Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "Eight shot dead in Nigeria jail break". The Sydney Morning Herald. 12 September 2007. Retrieved 26 December 2014.
- ↑ "BBC NEWS - Africa - Eight die in Nigeria 'jail-break'". 11 September 2007. Retrieved 26 December 2014.