Fatima Kyari Mohammed

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatima Kyari Mohammed
Rayuwa
Haihuwa Najeriya
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Matakin karatu Digiri
master's degree (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Permanent Observer of the Holy See to the United Nations (en) Fassara

Fatima Kyari Mohammed ita ce Daraktar din-din-din da ke lura da Tarayyar Afirka a Majalisar Dinkin Duniya.[1]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi digirin farko a fannin kera muhalli daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Najeriya, sannan ta yi digiri na biyu na Jami’ar Gudanar da Harkokin Kasuwanci daga Jami’ar Turai, sannan ta yi digiri na biyu a bangaren bunkasa tattalin arziki mai dorewa daga Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Zaman Lafiya, da kuma digiri na biyu na Kimiyyar kere-kere cikin aminci, tsaro, ci gaba da kuma sauya rikice-rikice daga Jami'ar Innsbruck, Austria.[2]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin nadin nata a matsayin Darakta na Dindindin na Kungiyar Tarayyar Afirka ga Majalisar Dinkin Duniya, Madam Mohammed ta kasance babbar Mashawarciya ta Musamman ga Kwamitin Kungiyar Kasashen Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ( ECOWAS ), tare da mai da hankali kan zaman lafiya da tsaro, hadewar yanki da ci gaban kungiya. . Kafin shiga kungiyar ECOWAS, ta kasance Babban Darakta a Yammacin Afirka Rikici da Tattaunawar Tsaro. Tun da farko, ta yi aiki a matsayin Manajan Shirye-shirye a Tawagar Tarayyar Turai zuwa Kasar Najeriya da ECOWAS; kuma a matsayin Manajan Gudanarwar Yanki don ayyukan Manufofin Tsaro a Nahiyar Afirka ta Yamma.[3]


Kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

An zabi Fatima ne don lambar yabo ta fitacciyar mace a cikin zaman lafiya, wanda kamfanin NCMG na duniya ya Bata.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "New Permanent Observer for African Union Presents Letter of Appointment | Meetings Coverage and Press Releases". www.un.org. Retrieved 2020-03-09.
  2. "Fatima Kyari Mohammed of Nigeria becomes new Permanent Observer for African Union". Sri Lanka News - Newsfirst (in Turanci). 2018-04-01. Retrieved 2020-03-10.
  3. "Africa House for a Fireside Chat with H.E. Ambassador Fatima Kyari Mohammed, African Union Permanent Observer to the United Nations". NYU Africa House (in Turanci). Retrieved 2020-03-10.