Fausat Adebola Ibikunle

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fausat Adebola Ibikunle
Rayuwa
Sana'a

Fausat Adebola Ibikunle ita ce ministar ma'aikatar gidaje da ci gaban birane a yanzu kuma itace babbar

mai Kula da Birane[1] da Bunkasa Jihar Kaduna (KASUPDA), Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad el-Rufai ne ya nada ta.[2][3][4][5]

Rayuwar farko da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Fausat, a jihar Kaduna. Ta karanci Gine-gine, sannan ta samu takardar shaidar digiri a jami'ar Ahmadu Bello inda ta kammala a shekara ta 1983.[2]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 1984, ta kuma yi aiki tare da Ma’aikatar Tsaro, sannan daga baya Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya. Ta kasance ashekara ta 2005, mataimakiyar darekta a Sashen Gina Jama’a. A shekara ta 2007, Fausat ta zama mataimakiyar darekta a Sakatariyar Kiwon Lafiya da Hidima a Babban Birnin Tarayya Daga baya ta zama kwamishina na Gidaje da Raya Birane.[6] [7]A yanzu haka ita ce babbar manaja na Hukumar Tsara Birane da Raya Kasa (KASUPDA) na Jihar Kaduna. [8] [9]

Manazartai[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "El-Rufai swears in commissioners". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2019-07-12. Retrieved 2020-11-09.
  2. 2.0 2.1 "El-Rufai nominates 11 Commissioners for Kaduna" (in Turanci). 2019-07-03. Retrieved 2020-11-09.
  3. "El-Rufai swears in new commissioners in Kaduna, sues for diligence". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-07-12. Retrieved 2020-11-09.
  4. "El-Rufai appoints Yoruba architect as commissioner". P.M. News (in Turanci). 2019-07-03. Retrieved 2020-11-09.
  5. IV, Editorial (2019-07-03). "Kaduna: El-Rufai appoints spokesman as internal security commissioner, 10 others". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2020-11-09.
  6. "Fausat Adebola Ibikunle". We Break the News as the Events Unfold! (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-19. Retrieved 2020-11-09.
  7. Tauna, Amos (2019-07-05). "Kaduna Assembly confirms 11 commissioners, appoints principal officers". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-11-09.
  8. https://www.pmnewsnigeria.com/2019/07/03/el-rufai-appoints-yoruba-architect-as-commissioner/
  9. https://www.blueprint.ng/kaduna-el-rufai-appoints-spokesman-as-internal-security-commissioner-10-others/

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

  • "Kaduna State Urban Planning and Development Agency (KASUPDA)". kasupda.kdsg.gov.ng. Retrieved 2020-11-09.