Nasir Ahmad el-Rufai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Nasir Ahmad el-Rufai
ɗan Adam
jinsinamiji Gyara
ƙasar asaliNijeriya Gyara
lokacin haihuwa16 ga Faburairu, 1960 Gyara
wurin haihuwaDaudawa Gyara
sana'aɗan siyasa Gyara
muƙamin da ya riƙeGovernor of Kaduna State Gyara
makarantaJami'ar Ahmadu Bello, University of London, John F. Kennedy School of Government Gyara
jam'iyyaPeople's Democratic Party Gyara

Nasir Ahmad el-Rufai ɗan siyasan Nijeriya ne. An haife shi a shekara ta 1960 a Daudawa, Arewacin Nijeriya (a yau a cikin karamar hukumar Faskari, a cikin jihar Katsina).

Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya ne daga shekara 2003 zuwa 2007. Gwamnan jihar Kaduna ne daga shekarar 2015 (bayan Mukhtar Ramalan Yero).

Farkon Rayuwa da Karatunsa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haife EL-Rufai a garin Daudawa dake karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina.[1] Mahaifinsa yarasu yana shekara 8.[2] An taimaka masa a karatun daga wani kawunsa dake zaune a Kaduna, kuma yatashi da rayuwarsa duka a arewacin Najeriya yayi.[2] Yayi karatun firamare a Kawo makarantar Firamari dake Kawo, Kaduna, da karatun sakandare a Kwalajin Barewa, inda yagama da sakamako a sama da sauran yan'ajinsu, inda ya lashe "Barewa Old Boys' Association Academic Achievement" Trophy a 1976.[3] A kwalejin Barewa dake Zaria, El-Rufai ya hadu da tsohon shugaban kasa Malam Umaru Yar'Adua wanda shine House Captain na Mallam Smith House inda nan ne dakin kwanan El-Rufai yake amatsayin sa na karamin dalibi wato junior.[4] Daga nan yaje Jami'ar Ahmadu Bello, dake Zaria, yafita da digirin Bachelor a Quantity Surveying da daraja mafi daukaka wato First Class Honors.[5] Ya kuma yi karatuttuka bayan nan a Harvard Business School da Jami'ar Georgetown.[6] Since leaving public service,[7] Nasir yayi karatun lauya da samun sakamakon LL.B digiri daga Jami'ar London, yafita a August 2008 da daraja na biyu wato Second Class Honours, Upper Division, da kuma digirin master's a fannin Public Administration daga John F. Kennedy School of Government, Jami'ar Harvard a watan Yuni 2009. Kuma ya karbi Kennedy School Certificate in Public Policy and Management wanda ya kwashe watanni 11 amatsayin Edward A. Mason Fellow in Public Policy and Management daga watan Yuli 2008 zuwa watan Yunin 2009.[8]

Farkon Aikinsa[gyara sashe | Gyara masomin]

El-Rufai ya kafa kamfani na kididdiga da kula da ayyukan Project a 1982 tare da wasu mutane uku.[9][2] Kamfanin na karbar ayyukan gine-gine da civil engineering projects a kasar Najeriya. Daga watan Nuwanba 1999 zuwa watan Yulin shekara ta 2003, shine Darekta Janar na Bureau of Public Enterprises kuma shine sakatare na National Council of Privatization inda ya jagoranci sayar da kamfanonin gwamnati da dama, tare dashi da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.[10] Yasamu nasara a kasuwancin gidaje a sakamakon cigaban da aka samu na karin gin-gine da amfani da filaye a Babban birnin tarayya wanda aka zarga da cin-hanci da rashin bin dokar asalin tsarin birnin.[11] tare da kafa Abuja Geographic Information System da kwashe watanni 12 amatsayin ministan Babban birnin tarayya, Abuja tazama na farko daga cikin biranen Najeriya wanda keda tsarin rijistan filaye na komfuta.[12][13] Tare da Shugaban kasa da mambobin Economic Management Team, karkashin jagorancin sa yaja ragamar canja fasalin tsarin aikin gwamnati wacce ta kwashe lokaci bata aiki sanadiyar mulkin soji.[14] A lokuta daban-daban sanda yake Minista, ya rika lura da Federal Ministries of Commerce (twice) and Interior.[15] El-Rufai ya rike kwamiti da dama, daga ciki itace wacce suka kafa tsarin mortgage a Nijeriya,[16] National ID card system for Nigeria,[17] Electric Power Supply Improvement and the sale of Federal Government real estate in Abuja.[18]

Siyasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Lokacin karshen mulkin shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban EFCC ya bayyana El-Rufai amatsayin "de facto No. 2 official", da samasa lakabin mataimakin shugaban kasa, musamman bayan rashin jituwar shugaban kasan da mataimakin sa. An yarda da cewa yarda da tabbaci da Obasanjo yake dashi ga El-Rufai yasa yan'siyasan Nijeriya jin haushin sa.[19]

Rayuwar Iyali[gyara sashe | Gyara masomin]

El-Rufai ya auri marubuciya Hadiza Isma El-Rufai. Wanda tare da ita ne, suka kafa Yasmin El-Rufai Foundation (YELF), wanda suka kaddamar dan tunawa da yar'su wacce ta rash a shekarar 2011.[20]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. "Archived copy". Archived from the original on 6 February 2010. Retrieved 2009-11-28. 
 2. 2.0 2.1 2.2 "Profile: Mallam Nasir el-Rufai". BBC News. 7 September 2004. 
 3. Bahaushe Mai Ban Haushi! (1 June 2009). "Bahaushe Mai Ban Haushi!: Yar’Adua: Great Expectation, Disappointing Outcome". Ibrahim-sheme.blogspot.com. 
 4. [1] webarchive |url=https://web.archive.org/web/20060721044351/http://www.nigeriafirst.org/docs/ministers_profiles.htm |date=21 July 2006
 5. "Nasir El Rufai". LinkedIn. 
 6. "Harvard Kennedy School". Hks.harvard.edu. 
 7. [2] webarchive |url=https://web.archive.org/web/20131109224644/http://www.whartonafricaforum.com/2008/speakers.html |date=9 November 2013
 8. http://thenationonlineng.net/el-rufai-radical-in-the-saddle/
 9. "OnlineNigeria.com – Nasir Ahmad el-Rufai". Nm.onlinenigeria.com. 
 10. http://en.newspeg.com/Nigeria-El-Rufai-Has-Zero-Tolerance-for-Corruption---Obj-3926799.html{{dead link|date=January 2018 |bot=InternetArchiveBot |fix-attempted=yes
 11. Peter-Omale, Funmi (2006-04-11). "Nigeria: Abuja Land Registry Nets N4bn in 2005 - El Rufai". This Day (Lagos). 
 12. "Civil Service Reform: Yayale loses out in Power game". Elombah.com. 20 September 2009. 
 13. Vincent Akanmode. "The Punch :: How Obasanjo granted el-Rufai the power to rule Abuja without the FCT ministry – Dr. Layi Ogunbambi". Punchontheweb.com. Archived from the original on 2 October 2011. Retrieved 18 October 2011. 
 14. [3] webarchive |url=https://web.archive.org/web/20090417054150/http://www.sunnewsonline.com/webpages/features/powergame/2009/feb/08/powergame-08-02-2009-004.htm |date=17 April 2009
 15. Oota, Andrew (2008-04-16). "Nigeria: Is El-Rufai Really Guilty?". Leadership (Abuja). 
 16. "independentngonline.com". www.independentngonline.com. 
 17. "Mallam Nasir el-Rufai | NigerianMuse". Nigerianmuse.com. 
 18. Ojeifo, Sufuyan (2008-04-11). "Nigeria: 75,000 Houses Demolished in Abuja Under El-Rufai". This Day (Lagos). 
 19. "naijadiscussion.com". naijadiscussion.com. Archived from the original on 9 October 2011. Retrieved 18 October 2011. 
 20. "I used to sing in the Catholic Church choir — Hadiza El-Rufai". Punch Newspapers (in en-US).