Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Ado-Ekiti
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Ado-Ekiti | |
---|---|
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Federal Polytechnic Ado Ekiti. |
Iri | institute of technology (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1977 |
fedpolyado.org |
Federal Polytechnic, Ado-Ekiti babbar makarantar fasaha ce a Ado Ekiti, Jihar Ekiti, Najeriya. Shugaban makarantar shi ne Engr. Dayo Hephzibah Oladebeye (Phd).[1][2] Makarantar tana kan hanyar Ado / Ijan Ekiti, Ado-Ekiti, Jihar Ekiti, Najeriya.
Tsarin Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Kwalejin Fasaha ta Tarayyar dake Ado-Ekiti tana ba da difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa,[3] da kuma takaddar shaida da masu karatun neman gogewa ta musamman a cikin: fasahar gine-gine, tsara birane da yanki, ilimin sanin kasa da lan an sabe, ilimi ƙididdigar bincike, fasahar injiniyan gidaje, injiniyarin ɗin albarkatun ƙasa da ma'adinai, fasahar injiniyan injina da lantarki, kimiyyar kwamfuyuta, fasahar abinci, kididdiga, Fasahar aikin Banki da Kudi, Ilimin Gudanar da Kasuwanci, Ilimin Fasahar Gudanar da Gidaje, da kuma Fasahar Ofishin Gudanarwa. Makarantar na da tsangayu biyar:
- Tsangayar Nazarin Kasuwanci
- Tsangayar Injiniyarin
- Tsangayar Nazarin Muhalli
- Tsangayar Kimiyya
- Nazarin Kwamfuta
- Tsangayar Noma da Fasahar Noma.
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
The Federal Polytechnic Ado ekiti
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "FPA Confirms Appointment of New Deans For its Four Schools". Federal Polytechnic, Ado-Ekiti. August 2017. Archived from the original on 2017-10-10. Retrieved 2017-10-09.
- ↑ "Ado-Ekiti Poly Staff Begin Indefinite Strike, Demand Rector's Sack". Africa Independent Television. 2015. Retrieved 2017-10-09.
- ↑ "History of FPA". Federal Polytechnic, Ado-Ekiti. Archived from the original on 2017-10-10. Retrieved 2017-10-09.