Jump to content

Fort Augustaborg

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fort Augustaborg
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaGhana
Yankuna na GhanaYankin Greater Accra
Coordinates 5°35′N 0°06′W / 5.58°N 0.1°W / 5.58; -0.1
Map
History and use
Opening1787
Heritage
Rushewar Fort Augustaborg a cikin 1890s.

Fort Augustaborg wani sansanin Danish ne a gabashin Gold Coast a Ghana a yau, wanda ke da nisan kilomita 15 daga gabas da Fort Christianborg kusa da Teshie a yau.[1]

An sanya wa katangar sunan Gimbiya Louise Augusta ta Denmark, an gina katangar ne a shekara ta 1787 don yaƙar hare-hare daga Daular Portugal.[2] Haka kuma an yi amfani da wurin a matsayin wurin cinikin bayi na Atlantic.[3] Shekaru biyar bayan haka, Denmark ita ce ƙasar Turai ta farko da ta kawar da cinikin bayi.[4]

A ranar 17 ga watan Agusta 1850, sansanin yana ɗaya daga cikin sansanin biyar na Danish da Sarauniya Victoria ta saya.[5]

Bayan samun ƴncin kai ga Ghana a shekarar 1957, sansanin ya zama mallakin sabuwar gwamnati. Tare da wasu sansanoni 32 da katanga a gabar tekun Ghana, Ganuwar Augusaborg, wuri ne na Tarihin Duniya na UNESCO.[6]

  1. Pocu, Kojo. "Forts And Castles In Ghana - Full List". Mr. Pocu Blog (in Turanci). Retrieved 2022-12-08.
  2. "Fort Augustaborg". NO CoVax Ghana-Net.com (in Turanci). Retrieved 2022-12-01.
  3. Juang, Richard M.; Morrissette, Noelle (2008-03-12). Africa and the Americas: Culture, Politics, and History [3 volumes]: Culture, Politics, and History (in Turanci). ABC-CLIO. ISBN 978-1-85109-446-2.
  4. "Ghana Museums & Monuments Board". ghanamuseums.org. Retrieved 2022-12-08.
  5. Y, Dr (2018-04-25). "Denmark and Slavery: Danish Forts and Possessions on the Gold Coast". African Heritage (in Turanci). Retrieved 2022-12-08.
  6. "Visit Ghana - Forts and Castles in Ghana". Visit Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-12-08.
  • Jerin manyan gidaje a Ghana