Jump to content

Francisca Ikhiede

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Francisca Ikhiede
Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna, 17 ga Janairu, 1996 (28 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a volleyball player (en) Fassara

Francisca Ikhiede (An Haife ta a ranar 17 ga watan Janairu 1996) 'yar wasan volleyball ce ta Najeriya wacce ke taka leda a kungiyar Customs ta Najeriya da kuma kungiyar kwallon raga ta mata ta Najeriya.

An haifi Ikhiede a Kaduna a shekarar 1996.[1] Ta taba bugawa kungiyar kwallon ragar hukumar kwastam ta Najeriya wasa.[2]

Ikhiede tana taka leda a kungiyar kwallon volleyball "b" ta bakin teku (Beach volleyball) ga kungiyar kwallon ragar mata ta Najeriya.[3] A farkon shekarar 2019 ta kasance a Yaoundé a Kamaru inda ita da Tochukwu Nnourge suka lashe lambar zinare a gasar kwallon ragar beach ta Camtel International. Sun samu nasara a wasan karshe duk da murnan da jama'a suka yi domin adawarsu ita ce ta Kamaru. [4]

Tawagar Najeriya ta zo ta biyu a lokacin da Kenya ta samu gurbin shiga gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2020 da aka dage. Kasashen Afirka hudu ne kawai suka tura tawaga zuwa gasar Olympics. [5] Tawagar Kenya ta kasance Yvonne Wavinya, Brackcides Agala, Phosca Kasisi da Gaudencia Makokha. Tawagar Najeriya ta sha kashi a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi a Morocco a 2021. [5] Tawagar Kenya ta Wavinga da Kasisi ta doke Tochukwu Nnoruga da Albertina Francis da ci 2-0 yayin da Agala da Makokha suka doke sauran 'yan Najeriya biyu na Ikhiede da Amara Uchechukwu da ci 2-1. [5]

  1. www.bvbinfo.com http://www.bvbinfo.com/ player.asp?ID=19378 . Retrieved 2021-07-20.
  2. "Francisca Ikhiede » clubs" . Women Volleybox . Retrieved 2021-07-20.
  3. "Beach V/ball: Nigeria women team to miss Tokyo Olympics" . ACLSports . 2021-06-27. Retrieved 2021-07-20.
  4. "Team Nigeria women's team wins beach volleyball championship in Cameroon" . The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News . 2019-01-01. Retrieved 2021-07-22.
  5. 5.0 5.1 5.2 volleyballworld.com. "Argentina, China, Cuba and Kenya take Olympic berths" . volleyballworld.com . Retrieved 2021-07-20.Empty citation (help)