Frederic Metcalfe
Frederic Metcalfe | |||||
---|---|---|---|---|---|
1955 - 1959
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 4 Disamba 1886 | ||||
ƙasa |
Birtaniya United Kingdom of Great Britain and Ireland | ||||
Mutuwa | 3 ga Yuni, 1965 | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Sidney Sussex College (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da cricketer (en) |
Sir Frederid William Metcalfe KCB (4 ga watan Disamba shekarar 1886 - 3 ga watan Yuni shekarar 1965) ma'aikacin gwamnatin Burtaniya ne. Ya kasnace tsohon magatakardan majalisar wakilai kuma shugaban majalisar wakilai ta farko .
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Metcalfe a cikin 1886 ga dangin WP Metcalfe na Ceylon da Hall Hall, Oxted . Yana da ilimin sa na farko a Wellington da Kwalejin Sidney Sussex, Cambridge sannan daga baya ya zama abokin girmamawa na kwaleji. [1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Ayyukan soja
[gyara sashe | gyara masomin]A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Metcalfe ya yi aiki tare da sojoji daga 1914 zuwa 1919 ya yi aiki tare da Bataliya ta Musamman ta 6 na Rifle Brigade .
Dan majalisa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 1919, Metcalfe ya sami nadin mukami a matsayin Mataimakiyar Magatakarda a Ma'aikatar Ma'aikata na Majalisar Wakilai, yana kan mukamin har zuwa 1930 kafin ya zama Mataimakin Babban Magatakarda na Biyu. Ya zama Mataimakin Magatakarda a 1937. A cikin 1948, an nada shi a matsayin magatakarda na Majalisar Wakilai har ya yi ritaya a watan Yuli 1954, ya gaji Lord Campion a wannan matsayin.
A shekarar 1955, Metcalfe ya zama kakakin majalisar wakilan Najeriya na farko bayan kaddamar da shi a ranar 12 ga watan Janairun 1955 ta John McPherson .
Rayuwar mutum
[gyara sashe | gyara masomin]Metcalfe ya auri Helen Goodman na Oxted.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Sir Frederic Metcalfe." Times [London, England] 5 June 1965: 12. The Times Digital Archive. Web. 4 Feb. 2016.
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |