Gasar Premier ta Ruwanda ita ce rukuni mafi girma na wasan kwallon kafa a Ruwanda. An kafa gasar a shekarar 1975. An sanya wa gasar suna Primus National Football League a cikin 2004 kuma daga shekarar 2009-10 zuwa 2012-13, bayan haka Turbo King ya karɓi jagoranci gasar.[1] An sauya wa gasar suna gasar Premier ta Azam Rwanda a kakar 2015 zuwa 2016 bayan da aka sanar da masu watsa shirye-shiryen talabijin na Tanzaniya Azam TV a matsayin masu daukar nauyin yarjejeniyar da ta kai dalar Amurka miliyan 2.35 na tsawon shekaru biyar.[2] Daga shekarar 2019 zuwa 2020 Azam TV ta sanar da kawo karshen kwantiraginta da kungiyar kwallon kafa ta Rwanda.[3]
↑Turbo King to take over league sponsorship" .
newtimes.co.rw. 13 September 2013. Archived from
the original on 1 February 2014. Retrieved 20
January 2014.
↑Azam TV to broadcast Rwanda's top tier league" .
Kawowo Sports. 26 August 2015. Retrieved 21
February 2016.
↑Rwanda - APR FC crowned league champions |
CAFOnline.com"