Jump to content

Goni Modu Bura

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Goni Modu Bura
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Mayu 1999 - Mayu 2003
District: Yobe East
Rayuwa
Haihuwa Jihar Yobe, 6 ga Janairu, 1960 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Goni Modu Zanna Bura tsohon sanata ne daga Jihar Yobe a Najeriya. An zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazaɓar Yobe ta Gabas a jihar Yobe a Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu a Najeriya, inda kuma ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar PDP. Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999.[1] Bayan ya hau kan kujerar majalisar dattawa a watan Yunin shekarar 1999 aka naɗa shi a kwamitocin ɗa’a, muhalli, lafiya, jiha da na ƙananan hukumomi da harkokin gwamnati.[2] Ya kasance ɗan takarar gwamnan jihar Yobe a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2003.[3]

  1. "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999". Psephos. Retrieved 2010-06-23.
  2. "Congressional Committees". Nigeria Congress. Archived from the original on 2009-11-18. Retrieved 2010-06-23.
  3. "Battle for PDP Tickets". ThisDay. 2002-12-22. Archived from the original on 2006-08-25. Retrieved 2010-06-23.