Grace Tabor
Grace Tabor | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Cuba (en) , 1873 |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mutuwa | 1973 |
Makwanci | Huntington (en) |
Karatu | |
Makaranta | New York School of Applied Design for Women (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Masanin gine-gine da zane |
Ina Grace Tabor an haife ta a 24 Maris shekarar 1874, a Cuba, New York ta mutu a 15 Oktoba shekarar 1971, [1] ta kasance ƴaran ƙasar Amurka landscape architect, mai zane, Marubuciya, kuma edita. Ta zamo ɗaya daga cikin mata na farko da suka bayyana kanta a matsayin mai zanen landscape architect.[2] An fi saninta da mawallafiya a kan batutuwan zanen landscape design, da aikin gona-(horticulture).[3] Ita ce marubucin littattafan lambu guda goma, yawancinsu an buga su tsakanin 1910 zuwa 1921.[4]
Tarihin rayuwa da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Grace Tabor a ranar 24 ga Maris 1874 a Cuba, New York. Ta yi karatu a Arts Students League da kuma New York School of Applied Design for Women duka a birnin New York.[3] Tabor ta sami horon aikin lambu a Arnold Arboretum na Jami'ar Harvard University.[4] A cikin 1905, Tabor, ta fara tsara rubutu da zane don wallafe-wallafen kamar a Mujallar The Garden Magazine da Country Life.[3] Ta zama editan Mujallar The Garden Magazine (daga baya The American Home); Mataimakin Daraktan, Makarantar Aikin Noma ta Jihar New York akan Long Island.[5]
Tabor, ta shafe yawancin rayuwarta (ta balaga) a yankin birnin New York.[2] Bayan ta yi ritaya, ta koma kudu, tana zama a jihohi daban-daban.[3]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 1914-1915 Tabor, ta fara aikin (landscape architecture) a asirce, musamman a kusa da birnin New York.[5] Ta gwammace ta tsara lambuna don masu matsakaicin kuɗin shiga maimakon masu arziki. Sakamakon haka, ba a rubuta gonakinta a cikin wallafe-wallafe ba.[3] Hukumar Lambun Yaƙi ta Ƙasa-(The National War Garden Commission) ta aika da ita yawon shakatawa na talla a lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya (WW1), don sha'awar samar da abinci a cikin Lambunan Yaƙi. Bayan yakin duniya na ɗaya, an naɗa ta shugabar sashin aikin gona na kwamitin Miss Anne Morgan na Faransa, kuma ta yi aiki a wannan matsayi a lokacin kasancewar kwamitin.[5]
A cikin 1920 Tabor ta rubuta wani littafi Come into the Garden inda ta yi magana game da yawan amfani da tsirai, tana ƙarfafa gwaiwar masu lambu.[6]
A cikin 1923 a matsayin ta na mai zane, mujallar Woman’s Home Companion ta nemi ta kafa Sashen Lambun a cikin wannan mujallar kuma ta yi aiki na ɗan lokaci a matsayin editanta.[5][7] Ta fara aiki a mujallar har zuwa 1941. Ta hanyar Woman's Home Companion, wanda a lokacin tana cikin manyan mujallun mata a ƙasar.[4] Ta bambanta tsohon da sabon salon aikin lambu tare da zane mai hoto na shimfidar wuri kafin da bayan gyare-gyare, ta sanya alamar "kafin" a matsayin "kuskure a cikin shimfidar wuri".[8] Rubutu da take ma Woman's Home Companion an ɗauke shi a matsayin gungun masu ba da shawara mata game da batun.[9]
Tabor ta rubuta littattafan lambu guda goma, yawancinsu an buga su tsakanin 1910 zuwa 1921.[3] Daga cikin muhimman littattafan akwai The Landscape Gardening Book (1911) da Come into the Garden (1921).[4] A cikin littafinta Old-Fashioned Gardening (1913) Tabor ta gabatar wa da masu karatu, lambuna na Amurka, Mulkin Mallaka.[4] A cikin 1951 Tabor ta buga littafinta na ƙarshe Making a Garden of Perennials.[2]
A cikin 1932 ta ba da shawarar dasa sabbin bishiyoyi miliyan 10 a Amurka don bikin cika shekaru biyu na haihuwar George Washington.[10]
Ta kasance edita na Mujallar Tsirrai, Fure da 'Ya'yan itace ta ƙasa.[3] Ta kuma ba da gudummawa sosai ga mujallar House and Garden, tana rubuta akan lambu a kowane wata da labarai masu zurfi game da aikin lambu.[11]
Wallafe-wallafen
[gyara sashe | gyara masomin]- 1911 – The landscape gardening book, wherein are set down the simple laws of beauty and utility which should guide the development of all grounds[12]
- 1911 – The garden primer; a practical handbook on the elements of gardening for beginners[13]
- 1912 – Making a garden to bloom this year[14]
- 1912 – Making the grounds attractive with shrubs[15]
- 1912 – Making the grounds attractive with shrubbery[16]
- 1912 – Making a bulb garden[17]
- 1913 – Old-Fashioned gardening; a history and a reconstruction[18]
- 1913 – Suburban gardens[19]
- 1916 – Wonderdays and wonderways through flowerland; a summer adventure of once upon a time[20]
- 1921 – Come into the garden[21]
- 1934 – Herbs in cooking[22]
- 1951 – Making a garden of perennials[23]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta mutu a shekarar 1973.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "IAWA Biographical Database". iawadb.lib.vt.edu. Retrieved 2020-01-17.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Birnbaum, Charles A.; Hughes, Mary V. (2005). Design with Culture: Claiming America's Landscape Heritage (in Turanci). University of Virginia Press. p. 9. ISBN 978-0-8139-2330-7.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 3.5 3.6 "Grace Tabor | The Cultural Landscape Foundation". tclf.org. Retrieved 2020-01-17.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 States (Project), Catalog of Landscape Records in the United; Initiative (Project), Historic Landscape (1993). Pioneers of American Landscape Design: An Annotated Bibliography (in Turanci). U.S. Department of the Interior, National Park Service, Cultural Resources. p. 119. ISBN 978-0-16-041974-4.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 "[Letter to Xavier L. Pellicer]". ufdc.ufl.edu (in Turanci). Retrieved 2020-01-17.
- ↑ "Every garden old is new again: Nostalgia plants for now". EP Henry (in Turanci). 2019-05-13. Retrieved 2020-01-17.
- ↑ "Harvesting the Vegetables". The Iowa Homemaker. 9 (3): 14. 1929.
- ↑ Foy, Jessica H.; Schlereth, Thomas J. (August 1994). American Home Life, 1880-1930: A Social History of Spaces and Services (in Turanci). Univ. of Tennessee Press. p. 201. ISBN 978-0-87049-855-8.
- ↑ Bradley, Patricia (2005-12-07). Women and the Press: The Struggle for Equality (in Turanci). Northwestern University Press. p. 102. ISBN 978-0-8101-2313-7.
- ↑ "Nightmare on Elm Streets". www.sactownmag.com. Retrieved 2020-01-17.
- ↑ Clayton, Virginia Tuttle (2000). The Once & Future Gardener: Garden Writing from the Golden Age of Magazines, 1900-1940 (in Turanci). David R. Godine Publisher. p. 29. ISBN 978-1-56792-102-1.
- ↑ Tabor, Grace (1911). The landscape gardening book, wherein are set down the simple laws of beauty and utility which should guide the development of all grounds (in Turanci). New York: McBride, Winston & Company. OCLC 1837042.
- ↑ Tabor, Grace (1911). The garden primer; a practical handbook on the elements of gardening for beginners (in Turanci). New York: McBride, Nast & Co. OCLC 3807532.
- ↑ Tabor, Grace (1912). Making a garden to bloom this year (in Turanci). New York: McBride, Nast & Company. OCLC 368753.
- ↑ Tabor, Grace (1912). Making the grounds attractive with shrubs (in Turanci). New York: McBride. OCLC 3189121.
- ↑ Tabor, Grace (1913). Making the grounds attractive with shrubbery (in Turanci). New York: McBride, Nast. OCLC 681232247.
- ↑ Tabor, Grace (1912). Making a bulb garden (in Turanci). New York: McBride, Nast & Company. OCLC 1838042.
- ↑ Tabor, Grace (1913). Old-fashioned gardening; a history and a reconstruction (in Turanci). New York: McBride, Nast & Company. OCLC 2901759.
- ↑ Tabor, Grace (1913). Suburban gardens (in Turanci). New York: Outing Publishing Company. OCLC 8912509.
- ↑ Tabor, Grace (1916). Wonderdays and wonderways through flowerland; a summer adventure of once upon a time (in Turanci). New York: R.M. McBride & Company. OCLC 8145805.
- ↑ Tabor, Grace (1921). Come into the garden (in Turanci). New York: The Macmillan Co. OCLC 2480351.
- ↑ Tabor, Grace (1934). Herbs in cooking (in Turanci). New York City: Woman's Home Companion. OCLC 51102570.
- ↑ Tabor, Grace (1951). Making a garden of perennials (in Turanci). New York: McBride. OCLC 1597679.