Gwari Abdu
Gwari Abdu (1805 – 1807) sarki ne na Haɓe a shekarar 1800, a masarautar Daura, daga shekarar 1805 zuwa 1807, wanda Mallam Ishi'aku ya karba mulki a hannunsa da taimakon Usman Dan Fodiyo.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Sarkin Daura Gwari Abdu ya gudu ya kuma bar Daura saboda samame da shehu Usman Dan Fodiyo ya kawo a Daura. Hakan yasa aka samu sabon sarki mai suna Mallam Ishi’aku, Abdu gwari ya gudu ne tare da tawagarsa, inda ya ɓoye a cikin Ƙasar hausa, da niyyan zai dawo ya ƙwace ƙasar Daura daga hannun Fulani.[1] Daga baya sai ya zauna a garin Yekuwa.[2] Yekuwa da Ƴardaji suna daga cikin manyan garuruwa a cikin Daura.[1] A garin yekuwa ne sarki Abdu ya zauna a matsayin sabon birninsa, wanda garin yana da tafiyar mil biyar zuwa Daura.[2]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Sarki abdu ya rasu a shekarar 1825.[3] bayan rasuwar shi a birnin Yekuwa, Ɗan uwanshi ne dama aka nada a matsayin magajin shi, bayan rasuwar Gwari Abdu, sai aka naɗa Ɗan uwanshi mai suna Lukudi, wanda dama shine magajinshi, sai Ɗan uwanshi ya cigaba da sarauta a yekuwa. Daura a ƙarni na 12, masarautar Daura tana sarautar fiye da garuruwa sittin.[2]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Miles, William F. S. (1994). Hausaland divided : colonialism and independence in Nigeria and Niger. Ithaca: Cornell University Press. ISBN 978-0-8014-7010-3. OCLC 624196914.
- Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710
- The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366