Hadiza Muhammad
Hadiza Muhammad | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Hajiya Hadiza Muhammad wacce aka fi sani da Hadiza Saima. Hadiza fitacciyar jaruma ce a masana'antar shirya fina-finai na Hausa (wato Kannywood). Tana taka rawa sosai cikin fina-finai a matsayin Mahaifiya.[1][2]
Farkon Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Hajiya Hadiza Muhammad a Unguwar Fage dake jihar Kano yar Fulani inda daga bisani ta koma rayuwa a Unguwar Birged dake cikin birnin na Kano. Ta yi karatun firamare a makarantar Gogoro Special Primary School, ta kuma yi sakandire bayan nan sai ta yi aure ta haifi yara guda biyu mace da namiji.[3][4]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Hajiya Hadiza ta fara sana'ar fim a shekarar 2010 a masana'antar shirya fina-finan Hausa (wato Kannywood) ta daukaka sosai a masana'antar kasancewarta hazikar jaruma mai masoya inda ake mata lakabi da bakya tsufa.
Jerin Fina-finai
[gyara sashe | gyara masomin]Ta fito a cikin fina-finai da dama kamar su:
- Buburwar Zuciya
- Dan Marayan Zaki
- Hajjaju
- Ummi
- Kalan dangi
- Labarina
- Alaqa
- A kashe da dai sauran su.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-12. Retrieved 2022-10-12.
- ↑ https://jackatapinch.com/hadiza-muhammad-saima-biography-net-worth-age/ Archived 2022-10-12 at the Wayback Machine
- ↑ https://instagram.com/hadizansaima
- ↑ http://hausafilms.tv/actress/hadiza_moh_d