Jump to content

Hanatou Ouelogo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hanatou Ouelogo
Rayuwa
Haihuwa 5 ga Augusta, 1978 (46 shekaru)
ƙasa Burkina Faso
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a judoka (en) Fassara
Nauyi 48 kg
Tsayi 151 cm

Konkiswinde Hanatou Ouelo (an haife ta a ranar 5 ga watan Agusta, 1978) 'yar wasan judoka ce ta Burkinabé, wacce ta taka leda a rukunin lightweight. [1] Ta samu lambar azurfa a gasar Judo ta Afirka a shekara ta 2004 da aka yi a birnin Tunis na ƙasar Tunisia, inda ta sha kashi a hannun Soraya Haddad na Aljeriya a wasan karshe. A lokacin da take da shekaru ashirin da shida, Ouelogo ta fara buga wasanta na farko a hukumance a gasar Olympics ta bazara a shekarar 2004 a Athens, inda tsohuwar 'yar wasa ta azurfa Lyubov Bruletova ta doke ta a wasan share fage na mata na kilogiram 48.

A gasar Olympics ta lokacin zafi ta 2008 da aka yi a nan birnin Beijing, Ouelo ta yi takara karo na biyu a ajin Lightweight na mata (48) kg). Ta sake yin rashin nasara a wasan share fage na farko a wannan karon, a hannun Kelbet Nurgazina ta Kazakhstan, wacce ta ci ippon kai tsaye ta kawo karshen wasan a minti ɗaya da ɗakika goma. [2]

  1. Evans, Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill; et al. "Hanatou Ouelogo". Olympics at Sports-Reference.com. Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 8 December 2012.
  2. "Women's Extra Lightweight (48kg/106 lbs) Preliminaries". NBC Olympics. Archived from the original on 21 August 2012. Retrieved 8 December 2012.