Hari a Izghe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHari a Izghe
Map
 10°59′00″N 13°18′00″E / 10.9833°N 13.3°E / 10.9833; 13.3
Iri aukuwa
attack (en) Fassara
Kisan Kiyashi
Kwanan watan 15 ga Faburairu, 2014
Adadin waɗanda suka rasu 106

Harin Izghe wani lamari ne na ta'addanci da ya faru a ranar 15 ga Fabrairu, 2014.[1]

Hari[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun shiga ƙauyen Izghe da ke jihar Borno da sanyin safiya inda suka kashe maza 105 da tsohuwa 1.[2][3]

Yanda harin ya faru[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu gungun mutane sun je wani ƙauye mai suna Izghe da ke jihar Borno, inda suka kashe mutane 106. Ƴan bindigar da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne. Sun "Kashe sama da mutane 100, ana zargin 'yan Boko Haram ne a harin da ya faru a karamin kauye da ake noma, Izghe, a Borno, Nigeria."[4]

Ɗaya daga cikin mutanen da ke da hannu a harin sai da ya tsallake shinge domin ceto rayuwarsa. "Wani wanda ya tsira daga harin ya haura katangar gidansa kuma ya yi ta rarrafe na tsawon mintuna 40 domin tsira."[5]

An kai harin ne da yammacin ranar Asabar, 16 ga Fabrairu, 2014. "Mazauna kauyen su ne aka kai wa harin da yammacin ranar Asabar."[4]

Inda aka kai harin shine ƙauyen Izghe, wani ƙauye a Najeriya. "Sun bi gida-gida don zaƙulo maza mazaunan da ke ɓoye." [5]

Wani hari a Konduga[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan wani ɓangare ne na hare-haren Boko Haram a watan Fabrairun 2014; kisan kiyashin Konduga ya faru a wannan rana shima.

Bayan nan[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ƴan kwanaki, an sake yin kisan kiyashi a ƙauyen.[6][7]

Ɓaraka[gyara sashe | gyara masomin]

An kai harin ne da nufin sanya al'ummar kasar shiga yaki. "A coci-coci inda ake kai hare-haren bama-bamai, mutane da yawa na ganin an yi yunƙurin haifar da baraka tsakanin Kirista da Musulmi da kuma watakila jefa Najeriya cikin yaƙin basasa wanda ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu na tsattsauran ra'ayin addini." "[8]

Hakan ya faru ne inda maharan suka shiga kauyen suka kashe fararen hula da dama.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Nigeria: EU HR Ashton strongly condemns mass killings in Izghe (retrieved 2014-02-June). The webpage of the EU Delegation to the UN. Archived 2013-08-23 at the Wayback Machine
  2. "Nigeria's Boko Haram 'in village massacre'". BBC News. 2014-02-16. Retrieved 2014-05-13.
  3. B’Haram murders 106 in fresh attack. Archived 2014-03-19 at the Wayback Machine February 17, 2014 by Emma Anya, Fidelis Soriwei and Kayode Idowu with agency report
  4. 4.0 4.1 Bourdon, J. (2014). Title: Latest Boko Haram attacks include Christian village. Retrieved from: https://www.mnnonline.org/news/latest-attacks-boko-haram-include-small-christian-village/
  5. 5.0 5.1 Abubakar, A. (2014). Title: Nigeria's Boko Haram targets muslim town and fishing village in latest attacks. Retrieved from: http://www.cnn.com/2014/02/16/world/africa/nigeria-boko-haram-attacks/
  6. Nigeria Boko Haram crisis: Anger over second Izghe raid. Retrieved 2014-02-June.
  7. Nigeria: Boko Haram attacks Izghe, Borno again. TVC News (retrieved 2014-02-June).
  8. Bavier, J. (2013). Title: Who are Boko Haram and why they Terrorizing Nigerian Christians? Retrieved from: https://www.theatlantic.com/international/archive/2012/01/who-are-boko-haram-and-why-are-they-terrorizing-nigerian-christians/251729/

Coordinates: 10°59′00″N 13°18′00″E / 10.9833°N 13.3000°E / 10.9833; 13.3000