Jump to content

Harin Bam a hedikwatar ƴan sandan Abuja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harin Bam a hedikwatar ƴan sandan Abuja
suicide car bombing (en) Fassara
Bayanai
Kwanan wata 16 ga Yuni, 2011
Wuri
Map
 9°01′42″N 7°29′53″E / 9.028203°N 7.498046°E / 9.028203; 7.498046

An yi amannar harin bam ɗin da aka kai hedkwatar ƴan sandan Abuja a shekarar 2011 shi ne harin ƙuna baƙin wake na farko a tarihin Najeriya.[1] Harin dai ya faru ne a ranar 16 ga watan Yunin 2011, lokacin da wani ɗan ƙuna baƙin wake ya tayar da bam a cikin harabar gidan Louis Edet da ke Abuja, hedkwatar rundunar ƴan sandan Najeriya .[2] Wataƙila (ɗan ƙuna baƙin waken) ya yi yunƙurin kashe Sufeto-Janar na ƴan sanda Hafiz Ringim, wanda ya bi ayarin motocinsa zuwa cikin harabar, amma jami'an tsaro sun tare shi kafin ya yi hakan. [3]

An tabbatar da mutuwar ɗan ƙuna baƙin waken da wasu jami’in tsaron kan hanya, ko da yake hukumomi sun ce ta yiwu an samu asarar rayuka har shida.[2]

Ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai harin.[4]

  1. Brock, Joe (17 June 2011). "Nigerian Islamist sect claims bomb attack: paper". Reuters. Archived from the original on 19 January 2012. Retrieved 17 June 2011.
  2. 2.0 2.1 Two die in Abuja bombing Archived 20 ga Yuni, 2011 at the Wayback Machine The Nation, 16 June 2011.
  3. Force hqtrs bombing: Suicide bomber was a foreigner — Interim report Vanguard, 17 June 2011.
  4. Nigeria's Boko Haram Islamists 'bombed Abuja police HQ'