Harin bam a Abuja, Disamba 2010
Appearance
| ||||
| Iri |
aukuwa bomb attack (en) | |||
|---|---|---|---|---|
| Kwanan watan | 31 Disamba 2010 | |||
| Wuri | Abuja | |||
| Ƙasa | Najeriya | |||
| Adadin waɗanda suka rasu | 4 | |||
| Adadin waɗanda suka samu raunuka | 26 | |||
| Perpetrator (en) | Boko Haram | |||
Harin da aka kai a Abuja a watan Disambar 2010, wani harin bam ne da aka kai a wani barikin sojoji da ke wajen birnin Abuja, Najeriya, a ranar 31 ga watan Disamban 2010. An kashe mutane huɗu ciki har da mace mai juna biyu, sannan wasu su 26 sun jikkata; a cewar ministan tsaro Adetokunbo Kayode, dukkan waɗanda suka mutu farar hula ne, haka kuma yawancin waɗanda suka jikkata.[1] Harin dai shi ne na biyu a Abuja cikin watanni uku, kuma shi ne na farko a kusa da wani bariki a ƙasar tun bayan komawar ta kan turbar dimokradiyya a shekarar 1999.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Barracks bomb claims 4 on New Year's Eve". TimesLIVE. South Africa. 1 January 2011. Retrieved 27 June 2012.
