Hassan Wayam
Appearance
Hassan Wayam | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Maradun, 1956 (67/68 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi |
Alhaji Hassan Wayam (an haife shi a shekarar alif 1956 ya kuma rasu a shekara ta alif 2020). ɗan asalin jihar Sokoto ne amma yayi duk rayuwarshi a garin Zaria jahar Kaduna. shahararren mawaƙin gargajiya ne na Hausa.[1]
Tarihin sa
[gyara sashe | gyara masomin]An kuma haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a ƙasar Maradun ta Jihar Zamfara, a cikin shekara ta 1956.[2]
Mahaifin sa, Malam Muhammadu, Babarbare ne. Mahaifiyar sa Halima, Bafulatana ce. Sana’ar mahaifinsa ita ce sassaƙa, to amma kuma wani lokaci ya kan yi wa Fulani kiɗan kotso jefi-jefi.[3]
Hijira
[gyara sashe | gyara masomin]Ali Barau ya kai Wayam Zariya a cikin shekara ta 1969, ya aje shi a gidan sa da ke Unguwar Kanawa. Duk yamma sai ya ɗauke shi ya kai shi.