Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta ƙasar Najeriya
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta ƙasar Najeriya | |
---|---|
Hukumar kare hakkin ɗan Adam |
Hukumar kare Haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa ( NHRC ), an kafa hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC), a shekara ta alif dari tara da casa'in da biyar 1995, kamar yadda dokar (NHRC), ta shekara ta dubu biyu da goma 2010, ta gyara. Hukumar tana aiki ne a matsayin wata hanya ta wuce gona da iri wacce ke kare hakkin bil'adama na al'ummar Najeriya. Tana sa ido a kan hakkin dan Adam a Najeriya, tana taimakawa wadanda aka take haƙƙin su, da kuma taimakawa wajen tsara manufofin gwamnatin Najeriya kan hakkin dan adam. [1]
Hukumar ta kasance mai himma wajen bincike da lura da al'amuran kare haƙƙin bil'adama da damar kafuwarta. [2][3] Amnesty International ta nuna damuwa game da tsoratar da Hukumar Kare Haƙƙoƙin Ɗan Adam ta ƙasa da rundunar 'yan sandan Najeriya ke yi a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu 2012.[4]
Sakataren zartarwa na yanzu shine Anthony O. Ojukwu Esq.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Hakkin Dan Adam a Najeriya
- Hukumar binciken take hakkin dan Adam ta Najeriya
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Agbamuche-Mbu, Mae (2015). "Nigeria and its Human Rights Commission, Articles". THISDAY LIVE. Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2015-03-28.
- ↑ "National Human Rights Commission". INFORMATION NIGERIA. Retrieved 2015-03-28.
- ↑ "Nigeria: End police intimidation of National Human Rights Commission". Amnesty International. 2012-04-13. Retrieved 2015-03-28.
- ↑ Ofeibea Quist-Arcton (2015-03-27). "As Nigeria Votes, The Specter Of Boko Haram Hangs Over The Election". NPR - Parallels. Retrieved 2015-03-28.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa, shafin hukuma