Jump to content

Anthony Ojukwu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anthony Ojukwu
Rayuwa
Haihuwa 1959 (64/65 shekaru)
Sana'a

Anthony Okechukwu Ojukwu Lauyan Najeriya ne Kuma Babban Sakatare na Hukumar Kare Haƙƙoƙin Ɗan Adam ta Najeriya, wata cibiya mai zaman kanta ta kasa don inganta, da kariya da tabbatar da haƙƙin ɗan Adam a Najeriya . A cikin shekara ta 2021, an naɗa shi Babban Lauyan Najeriya (SAN).[1][2][3][4][5]

Ojukwu ya samu digirinsa na farko (LLB) a fannin shari'a a Enugu Campus a Jami'ar Najeriya.A shekara ta alif ɗari tara 1998, ya kammala digirinsa na biyu (LLM) a fannin shari'a a Jami'ar Legas, Akoka.Ojukwu ya kuma kammala shirin horar da ƴancin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa (IHRTP) a ƙasar Kanada a shekarar 2007.

Sana'a/Aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Anthony Okechukwu Ojukwu a matsayin Sakataren Gudanarwa/Shugaba na Hukumar sakateriya ta Ƙasa (NEC) a Jihar Imo.A shekarar 2001, an naɗa shi a matsayin mataimaki na musamman ga tsohon babban sakataren hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa Dr Bukhari Bello, mni, MFR.Daga baya an zaɓi Ojukwu tare da naɗa shi a matsayin babban sakataren hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa shugaba Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi a watan Disamba, 2021.[6]

  1. "Missing General: NHRC advises army on human rights violation". The Sun Nigeria (in Turanci). 2018-10-15. Retrieved 2022-03-30.
  2. siteadmin (2022-03-23). "Disgraced DCP Abba Kyari Has Many Cases With Us, Police Authorities Shielded Him Since 2008 – Nigerian Agency, NHRC Reveals". Sahara Reporters. Retrieved 2022-03-30.
  3. "Overview - National Human Rights Commission". www.nigeriarights.gov.ng. Retrieved 2022-03-30.
  4. "LPPC elevates 72 lawyers to SAN rank". Vanguard News (in Turanci). 2021-10-22. Retrieved 2022-03-30.
  5. "FULL LIST: NHRC boss among 72 lawyers named senior advocates of Nigeria". TheCable (in Turanci). 2021-10-21. Retrieved 2022-03-30.
  6. "Senate kicks as Anthony Ojukwu resumes as NHRC boss". TVC News (in Turanci). 2018-03-01. Retrieved 2022-03-30.