Jump to content

Ibeno Beach

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibeno Beach
bakin teku, tourist attraction (en) Fassara da natural heritage (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1996
Nahiya Afirka
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 4°32′26″N 8°00′11″E / 4.540624°N 8.003107°E / 4.540624; 8.003107
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Akwa Ibom
Ƙananan hukumumin a NijeriyaIbeno
Ibeno Beach

Bakin Tekun Ibeno na ɗaya daga cikin rairayin bakin teku dake gaɓar Tekun Atlantika gami da gaɓar Ibeno. Wurin ne bakin teku mafi tsayi a yammacin Afirka[1][2] Kogin Qua Iboe shine babban wurin da ke bakin Tekun Ibeno. Tekun Ibeno ya kai kimanin kilomita 30 daga Ibeno zuwa garin James da ke gabar tekun Atlantika a jihar Akwa Ibom a kasar Najeriya. Wurinne mafi kyawun yawon buɗe ido na bakin ruwa a Jihar Akwa Ibom, Akwai yanayi mai kyau a ƙayataccen bakin tekun, ga masu zuwa yawon buɗe ido. Kama daga, wuraren; wasanni na ruwa, ƙwallon ƙafa na bakin teku da kuma hawan kwale-kwale.[3]

Kogin Ibeno yana cikin ƙaramar hukumar Ibeno, jihar Akwa Ibom a kudu maso gabashin kasar Najeriya, wacce aka saka mata sunan kogin.[4] Bakin tekun na ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido a Najeriya. A watan Yunin shekarar 2010, an sami rahoton malalar mai a bakin tekun.[5]

  1. unwana (2021-03-08). "Ibeno Beach: Everything You Need to Know". Awajis (in Turanci). Retrieved 2021-09-13.
  2. "Ibeno Beach: So white, so natural". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 3 January 2015. Retrieved 7 March 2015..
  3. Umoh et al., 2022. "Glycerol dialkyl glycerol tetraether signatures in tropical mesotidal estuary sediments of Qua Iboe River, Gulf of Guinea". Journal of Organic Geochemistry 170, 104461.
  4. "5 Beautiful Places You Should Visit In Akwa Ibom". Nigerian Bulletin - Trending News & Updates. Retrieved 7 March 2015.
  5. "Fresh oil spill exxonmobi's qua iboe oil field ravages akwa-ibom. Coastline". Sahara Reporters. Retrieved 7 March 2015.