Ibillo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibillo

Wuri
Map
 7°26′14″N 6°04′14″E / 7.43732613°N 6.07048277°E / 7.43732613; 6.07048277
Yawan mutane
Harshen gwamnati Turanci
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Ibillo Gari ne mafi girma a karamar hukumar Akoko-Edo jihar Edo Najeriya. Ibillo na kewaye da garuruwa/kauyuka da dama da suka hada da Ikiran Oke, Imoga, Ekpesa da Lampese wadanda dukkaninsu na cikin al’ummomi Ashirin da biyu ne da suka ginayankin al'ummar Okpameri, duk a karamar hukumar Akoko Edo da hedikwatar karamar hukumar Igarra.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Abubuwa Kaɗan ne aka rubuta game da asalin mutanen Ibillo, amma, a al'adar baka, an yi imanin cewa mutanen sun yi hijira daga masarautar Benin.Mutanen sun tsunduma cikin irin sana'o'i kamar noma, ciniki, sarrafa itace da kuma tukwane. Ƙasar tana da albarka kuma tana da babbar kasuwa dangane da sauran al'ummomin Akoko-Edo. Kasuwar tana kan titin Ibillo – Abuja express way. Ibillo ya rabu sassa hudu kuma ana juya mulki a cikin waɗannan sassan.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]